NDA: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Makarantar Horar da Sojojin Najeriya

 

Hukumar makarantar NDA ta tabbatar da harin da ‘yan bindiga suka kai mata a safiyar yau Talata.

Kakakin NDA, Manjo Bashir Jajira ne ya tabbatar da lamarin inda ya sha alwashin cewa za su bi sawun maharan.

Ya kuma tabbatar da kisan jami’ai biyu tare da sace daya.

Makarantar horar da Sojojin Najeriya (NDA) ta tabbatar da kisan jami’ai biyu a lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari barikin a ranar Talata, 24 ga watan Agusta.

Sanarwar da jami’in hulda da jama’a na makarantar, Manjo Bashir Jajira ya fitar, ya ce ‘yan bindigar sun sace wani jami’i, jaridar Daily Trust ta rawaito.

NDA ta bayyana cewa tana kan bin diddigin ‘yan fashin da suka yi kutse a tsarin tsaronta, jaridar Punch ta rawaito.

Hadimin Shugaban kasa, Buhari Salau ya wallafa sanarwar kakakin rundunar a shafinsa na Facebook, inda yake cewa:

“Da safiyar yau wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi kutse a tsarin tsaro na Kwalejin sojojin Najeriya. A yayin wannan abin takaici, mun rasa jami’ai biyu kuma an sace daya.

“Makarantar tare da hadin gwiwar Babbar Runduna ta 1 ta Sojojin Kasa da kuma Rundunar Horo ta Sojin Sama da sauran hukumomin tsaro da ke Jahar Kaduna na bin sawun masu garkuwar a yankin domin kubutar da wanda aka yi garkuwa da shi.

“Kananan hafsoshi da ke samun horo da sauran al’umma da ke zaune a barikin NDA suna cikin aminci. Muna ba wa jama’a tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a cafke ’yan bindigar a kubutar da sojan.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here