‘Yan Bindiga Sun Kaiwa ‘Yan Sanda Farmaki a Jahar Delta

 

Wasu ‘yan bindiga sun farmaki yan sanda ya yin da suke tsakar sintiri a garin Ashaka, karamar hukumar Ndokwa, jahar Delta.

Maharan sun hallaka wani ƙaramin sufeta sannan suka babbaka ma motar yan sandan wuta.

Jami’i mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jahar Delta, Mr. Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma yace an kashe musu jami’i daya.

Wasu yan bindiga sun farmaki yan sanda ya yin da suke sintiri a garin Ashaka, karamar hukumar Ndokwa ta gabas a jahar Delta.

Yan bindigan sun caka ma ɗaya daga cikin yan sandan wuƙa wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa kuma suka jikkata wasu sannan suka babbaka ma motar da yan sandan ke sintiri da ita wuta.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa maharan sun kori ‘yan sandan da tsiya kuma suka yi gaba da makaman su.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Talata, a wani yanki na garin Ashaka.

Duk da cewa babu wani cikakken bayani akan abunda yafaru zuwa yanzun, amma an tabbatar da mutuwar sufeta mai suna Musa wanda suka caka ma wuƙa.

Wata majiya da ta umarci a sakaya sunanta ta bayyana ma jaridar Vanguard cewa: “Yan bindigan sun taho ne akan mota, suka farmaki yan sandan da suka fito sintiri a yankin.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here