Harajin Basu Kariya: ‘Yan Bindiga Sun Karbi N19m da Kwale-Kwale a Kauyukan Zamfara

 

Yan bindiga suna cigaba da cin karensu babu babbaka a wasu yankuna na Jihar Zamfara da sauran jihohin arewa maso yamma da tsakiya.

Rahotanni sun nuna cewa yan ta’addan sun karbi makuden kudi har Naira miliyan 19 har da kwale-kwale daga mutanen wasu kauyuka a Anka, Jihar Zamfara.

Wani shugaban al’umma a Anka ya tabbatar da lamarin yana mai cewa ba sabon abu bane domin dan mutanen ba su biya ba, za su zauna lafiya ba.

Zamfara – Kimanin garuruwa 14 a Jihar Zamfara sun yi karo-karo sun bawa yan ta’addan da ke Anka da Bukkuyum Naira miliyan 19 da kwale-kwale a harajin basu kariya.

Wani mai wallafa labarai, Yusuf Anka, wanda shima dan garin ne ya shaidawa Premium Times cewa garuruwa da dama a Anka suna tara kudin kariyar su biya yan ta’adda.

Ya ce yan ta’addan sun kakabawa garuruwan harajin daf da za a shigo damina.

Mr Anka ya ce mazauna garuruwan ba su da wani zabi illa tara wannan kudin domin gudun kada yan ta’addan su kawo musu hari yayin aiki a gonakinsu ko ma a gidajensu.

An wanda ya wallafa bidiyon bincike kan ta’addanci a baya-bayan nan mai taken ‘The Bandits Warlords of Zamfara’ ya ce:

“Dukkan garuruwan na karkashin Anka ne kuma an umurci su tara kudi don kariya. Wasu garuruwan sun biya kudinsu watanni biyu da suka gabata.Amma jimilar kudin ya kai Naira miliyan 19.” Ya ce mutanen garin Yar Sabaya ne suka siya kwale-kwalen. Rafi guda biyu ne suka zagaye garin Anka sannan akwai wasu kananan rafin a kewaye da shi.

Mr Anka ya kara da cewa:

“Yan bindigan sun umurci garuruwa daban-daban su tara musu kudi saboda su kyalle su suyi aiki a gonakinsu ba tare da kai musu hari ba. Ba wannan ne karon farko da suke biyan harajin ba.”

dadin harajin da kauyukan na Zamfara suka biya – Yusuf Anka

Ba bada sunayen kauyukan da suka biya kudi da adadin da suka biya kamar haka:

Jargaba N1.6m, Birnin doki N1m, Tangaram N1.5m (daga baya suka kara N2.5m), Jarkuka N1.5m, Tuntuja N500,000, Tsafta N1m, Tudun magaji N2m, Kadaddaba N820,000, Tudun kudaku N950,000, Gargam N1m, Kwanar Maje N900,000, Yar tumaki N1m, Bawar Daji N1.7m, Tungar Liman N6m da Makakari N430,000. Wani jagoran al’umma ya tabbatar da biyan harajin Wani jagoran al’umma a Anka wanda ya nemi a boye sunansa saboda tsaro ya ce sun san da batun biyan harin da yan ta’addan suka kakabawa mutane.

Wani jagoran al’umma ya tabbatar da biyan harajin

Wani jagoran al’umma a Anka wanda ya nemi a boye sunansa saboda tsaro ya ce sun san da batun biyan harin da yan ta’addan suka kakabawa mutane.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here