‘Yan Bindiga Sun Kashe Tsohon Sojan Sama, AVM Muhammad Maisaka
Rundunar ‘yan sandan jahar Kaduna sun tabbatar da kisan tsohon sojan sama, AVM Muhammad Maisaka da wasu ‘yan bindiga su ka yi har gidan sa da ke Rigasa, karamar hukumar Igabi da ke Kaduna.
Jami’in hulda da jama’an yankin, ASP Muhammad Jalige ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce abin ya auku ne da safiyar ranar Talata.
Ya kara da bayyana yadda har mai gadin sa ya samu miyagun raunuka sakamakon farmakin wanda bayan kwamishinan ‘yan sandan jahar, Mudassiru Abdullah ya tura jami’an sa wurin cikin gaggawa.
Kaduna – Rundunar ‘yan sandan jahar Kaduna sun tabbatar da kisan babban sojin sama mai murabus, AVM Muhammad Maisaka, da ‘yan bindiga su ka yi a gidan sa da ke Rigasa, karamar hukumar Igabi da ke jahar.
Read Also:
Jaridar The Nation ta ruwaito yadda jami’in hulda da jama’an rundunar na jahar, ASP Muhammad Jalige ya tabbatar wa da NAN aukuwar lamarin ranar Talata a Kaduna.
Yadda lamarin ya faru
Jalige ya bayyana yadda lamarin ya faru da safiyar Talata, sannan har mai gadin gidansa ma ya raunana sakamakon harin.
Ya ce bayan isar labarin wurin kwamishinan ‘yan sandan jahar, Mr Mudassiru Abdullah ya umarci ‘yan sandan yankin suyi gaggawar isa wurin da lamarin ya auku.
A cewarsa:
“An kai gawar sa ma’adanar gawawwakin da ke asibiti yayin da aka zarce da mai gadin gidan sa zuwa asibiti don duba lafiyar sa.”
Ya kara da cewa za su bayyana bayanai daki-daki akan yadda lamarin ya auku nan ba da jimawa ba.
Jalige ya bukaci mazauna Kaduna da suyi gaggawar gabatar wa jama’an tsaro bayanai masu amfani da zasu bayar da damar kama wadanda suke da alhakin yin wannan aika-aika.