An Tsige Kakakin Majalisar Imo, Paul Emeziem

Ƴan majalisar jahar Imo sun tsige kakakin majalisar Paul Emeziem a zaman da majalisar ta yi a ranar Litinin.

Ƴan majalisa 19 ne suka tsige shugaban majalisar daga cikin ƴan majalisar jahar 27.

A cikin takardar da aka karanta a zauren majalisar, ƴan majalisar sun ce sun tsige Mista Emeziem ne bisa zarge-zargen da suka haɗa da nuna rashin ɗa’a da cin mutuncin ofishinsa da kuma babakere.

Ƴan majalisar sun kuma zaɓi sabon kakakin majalisa Honarabul Kennedy Ibe.

Ko a watan Nuwamban bara ƴan majalisar sun tsige kakakin majalisar ta Imo, Mista Chiji Collins.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here