‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Dan Sanda 1, Sun yi Garkuwa da Mutane 23 a Jahar Kaduna

 

‘Yan bindiga sun hallaka sifetan ‘yan sanda sannan sun yi garkuwa da mutane 23 a wani farmaki da suka kai karamar hukumar Chikun.

An samu rahotanni a kan yadda ‘yan bindigan suka yi ta harbe-harbe a kauyen yayin da jama’a suka yi ta gudun neman tsira.

Ganau sun tabbatar da yadda suka yi asubancin kai hari Unguwan Maje da Unguwan Laka da ke karamar hukumar a ranar Laraba.

Kaduna- ‘Yan bindiga sun yi ajalin wani sifetan ‘yan sanda sannan sun yi garkuwa da mutane 23 sakamakon wani hari da suka kai Unguwan Maje da Unguwan Laka da ke karamar hukumar Chikun a jahar Kaduna.

TheCable ta fahimci yadda ‘yan bindigan suka kai farmakin da safiyar ranar Laraba.

An samu bayanai a kan yadda suka yi ta harbe-harbe ‘yan kauyen suna gudun neman tsira, TheCable ta rawaito.

Wani ganau ya ce:

“Da farko sun fara kai farmaki Unguwan Maje ne, inda suka yi garkuwa da mutane 15 wanda yawancin su mata ne da yara.

“Daga baya suka nufi Unguwan Laka inda suka hallaka wani sifetan ‘yan sanda, Joshua Markus daga zuwan sa ziyarar ‘yan uwansa tun daga jahar Rivers.

“Yan bindigan sun yi garkuwa da mutane 7 ciki har da mata da diyar wanda suka hallaka.”

Wani soja mai murabus, wanda dan Unguwan Laka ne ya samu nasarar tserewa da iyalin sa dakyar. Sai dai sun babbaka motarsa da babur dinsa.

An ajiye gawar sifetan a asibitin Saint Gerald Catholic da ke cikin Kaduna.

Da aka nemi jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan yankin, Mohammed Jalige, ya ce bai san da faruwar lamarin ba.

Amma ya yi alkawarin bincike a kai, kawo lokacin rubuta rahotan nan, ba a samu jin komai daga bakinsa ba.

Jahar Kaduna ta na daya daga cikin jahohin da ke fama da matsalolin rashin tsaro da kuma garkuwa da mutane har da hallaka su kusan kullum.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here