‘Yan Bindiga Sun Kashe Limami da Sarkin Yaki a Jahar Kaduna
Kungiyoyin yan ta’adda a yankin arewa maso yamma na ci gaba da yin barna a garuruwa.
Musamman jihar Kaduna, na ci gaba da fuskantar hare-haren yan bindiga, garkuwa da mutane da kuma ayyukan ta’addanci daban-daban.
Kisan baya-bayan nan da aka yi shine na wasu shugabanni biyu wadanda kungiyoyin ta’adda suka halaka a jihar Kaduna.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wasu da ake zaton yan bindiga ne sun kai hari kauyen Kawan Rafi da ke karamar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna sannan suka kashe Danleeman sah, babban limamin kauyen.
A cewar rahoton, yan bindigan sun kai farmaki gidan marigayin inda suka harbe shi, sannan suka bar shi a wajen ba tare da sun dauki komai ko satar wasu mutanen ba.
Read Also:
An tattaro cewa an alakanta kisan mlamin da da’awarsa ta bayyana tsagwaran adawa a kan yadda ’yan bindiga ke kashewa da garkuwa da mutane a yankin.
Hakazalika, wasu masu garkuwa da mutane sun kashe Sarkin Yakin a Godogodo, Mista Yohanna Abu.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya tabbatar da kisan jagororin biyu a cikin wata sanarwa.
Moses Baba ya rubuta a shafin Facebook:
“Ku kare kanku, Najeriya tamkar iyalai ne da ba su da iyalai. Ku kare kanku.”
Hashim Nyabali ya rubuta:
“Wadannan mutanen Boko Haram ne, babu wasu yan bindiga.”
Emmanuel Nwanneh ya rubuta:
“Idan kayi magana game da hauhawan rashin tsaro a kasar nan, wasu yan kashenin Buhari za su kare shi sosai. Wannan ya zarce siyasa, addini ko kabilanci.”