Sabon Hari: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3 a Jahar Kaduna

 

Wasu ‘yan bindiga sun sake kai sabon hari a ƙaramar hukumar Zangon Kataf dake kudancin Kaduna.

Maharan sun kashe aƙalla mutum uku tare da jikkata wata mata, sannan suka kona mota guda ɗaya.

Hakimin Gora, Mr. Elias Gora, shine ya bayyana haka, yace lamarin ya faru da daren ranar Lahadi.

Kaduna – Aƙalla mutum uku suka rasa ransu a wani sabon hari da yan bindiga suka kai kauyen Gora Gida, karamar hukumar Zangon Kataf, jahar Kaduna.

Da yake magana da dailytrust, Hakimin Gora, Mr Elias Gora, yace yan bindiga sun kai harin ne da misalin karfe 11:00 na daren ranar Lahadi.

Ya kara da cewa wata mata ta samu raunin harbin bindiga sannan kuma maharan sun kona mota guda ɗaya.

Mr. Gora ya kara da cewa mutum biyu daga cikin waɗanda aka kashe sun kasance mahaifi ne da ɗansa.

Hakimin yace:

“Maharan sun kai harin ne da misalin karfe 11:00 na daren ranar Lahadi, inda suka kashe mahaifi da ɗansa da kuma wani mutum ɗaya.”

“Yan bindiga sun harbi wata mata ɗaya sannan kuma sun kona mota guda ɗaya a yayin harin.”

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Kakakin rundunar yan sanda reshen jahar Kaduna, ASP Muhammed Jalige, ya ƙi daga kiran wayar da ake masa don jin ta bakinsa.

Har zuwa yanzun da muke kawo muku wannan rahoton hukumar yan sanda ba ta fitar da wata sanarwa game da harin ba a hukumance ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here