‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Sama da 300 a Jahar Neja

 

Sanata mai wakiltar mazabar Neja ta gabas, Mohammed Sani-Musa, ya bayyana yadda ‘yan bindiga suka hallaka fiye da mutane 300.

A ranar Talata, ya bayyana yadda suka janyo a kalla mutane 3000 suka rasa gidajen su a mazabar sa cikin watanni kadan da suka gabata.

Ya bayyana hakan ne a wata takarda a Minna, inda ya kwatanta ayyukan ‘yan bindigan a matsayin mugunta da zalinci.

Niger – Sanata mai wakiltar Neja ta arewa a majalisar tarayya, Mohammed Sani-Musa, a ranar Talata ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun hallaka fiye da rayuka 300 sannan sun hana fiye da mutane 3000 zama a gidajensu a cikin mazabar sa cikin watanni kadan da suka gabata.

Daily Nigerian ta rawaito cewa, a wata takarda da Sani-Musa ya saki a ranar Talata a Minna ta jahar Neja, ya kwatanta ayyukan ‘yan bindigan a matsayin zalunci da mugunta ga dan Adam.

A cewar sa:

“A cikin watanni biyu da suka gabata, a kalla mutane 3000 ne suka rasa gidajensu suka koma zama a sansanin ‘yan gudun hijira ,sannan sun yi asarar dukiyoyin su masu yawan gaske ta hanyar kwace ko kuma a lalata su.

“Abin akwai tashin hankali kuma a haka suka kara afkawa garuruwan da ke karamar hukumar Shiroro ta mazabar a makon da ya gabata inda suka yi wa mutane 20 yankan rago.

“Sun hallaka ‘yan kauyen nan tamkar tumaki, abu ne da bai kamata a cigaba da amincewa da shi ba. Don haka dole ne mu tashi tsaye mu yi iyakar kokarin ganin an kamo su an yanke musu hukunci.

Sanatan ya yi kira a kan kawo karshen ta’addanci a garuruwa inda yace ya kamata gwamnati ta mike tsaye ta tsare rayukan jama’an karamar hukumar Shiroro da sauran bangarorin mazabar Neja ta gabas, Daily Nigerian ta rawaito.

“Yanzu mutanen mu sun dena zuwa noma gonakin su saboda ta’addanci,” a cewar sa.

Ya kuma roki gwamnatin tarayya ta kawo tsaro a bangaren Bass, Magami da garin Kukokki inda da aka turo jami’an tsaro amma kwanaki aka karbe su. Hakazalika, akwai bukatar sansanin sojoji a tsakanin karamar hukumar Shiroro da jahar Kaduna.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here