‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 4 Masu Gina Matatar Mai a Jahar Imo

 

Akalla ma’aikatan kamfanin Injiniyanci na Lee hudu ne aka tabbatar sun mutu bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai musu harin.

kwanton bauna da safiyar Litinin 16 ga watan Agusta a yankin Assa da ke karamar hukumar Ohaji/Egbema ta jahar Imo.

Wakilin jaridar Punch ya tattaro cewa ma’aikatan man suna kan hanyarsu ta wucewa zuwa wurin gina matatar mai a yankin Assa ne lokacin da ‘yan bindigan suka bude musu wuta.

Yayin da hudu suka mutu nan take, wasu sun samu munanan raunuka sakamakon harbin bindiga.

Wata majiya daga kauyen ta shaida cewa kamfanin na gina matatar mai ne a yankin.

Shugaban Majalisar Matasan Ohaji na kasa, Emmanuel Ugorji, ya tabbatar da faruwar harin ga manema labarai.

Ya ce wasu shugabannin al’umma da jami’an tsaro, ciki har da shi, sun ziyarci wurin don ganewa idonsu.

Da yake yin kira ga gwamnati kan cewa ta karfafa tsaro a yankin, shugaban matasan ya ce ‘yan bindigar na ta addabar yankin a cikin ‘yan kwanakin nan.

Karin bayani na nan tafe…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here