‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 4 a Harin da Suka Kai Jahar Katsina

 

Miyagun ‘yan bindiga sun kai hari Kauyen Tsayau, karamar hukumar Jibiya da daren ranar Litinin.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kashe aƙalla mutum 4 tare da jikkata wasu 7 yayin harin.

Mazauna ƙauyen sun koka matuka kan yadda miyagun suka ɗauki tsawon lokaci suna ta’adi ba tare da an kawo ɗauki ba.

Katsina – Wasu yan bindiga sun sheke aƙalla mutum 4 a kauyen Tsayau, karamar hukumar Jibiya, jahar Katsina, ranar Litinin.

Dan majalisa mai wakiltar Jibiya a majalisar dokokin jahar shine ya tabbatar da haka ga Premium times.

Yace yan bindigan sun jikkata wasu mutum 7 tare da yin awon gaba da wasu da dama a yayin da suka kai mummunan harin.

Yaushe aka kai harin?

Wata majiya daga yankin da lamarin ya faru ta bayyana cewa maharan sun farmaki garin ne da misalin karfe 7:30 na dare ɗauke da muggan makamai.

Majiyar tace:

“Maharan sun shigo da misalin karfe 7:30 na dare ɗauke da manyan bindigu. Daga isar su suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi, a wannan lokaci ne suka bindige mutum 4.”

Mazauna ƙauyen sun bayyana sunayen waɗanda aka kashe da suka haɗa da, Umma Ta-malam, Jamilu Ibrahim, Amira Ibrahim, da kuma Zainab Wada.

Wane mataki jami’an tsaro suka ɗauka?

Majiyar ta kara da cewa sai bayan miyagun sun gama aikata ta’adin sun fece sannan jami’an tsaro suka kariso kauyen.

Mazauna Ƙauyen sun koka kan yadda maharan suka ci karansu babu babbaka na tsawon awa ɗaya ba tare da an kawo ɗauki ba duk kuwa da kiran gaggawa da suka yi wa sojojin Gurbi, tafiyar Kilomita ɗaya zuwa Tsayau.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here