Abubuwa 5 Game da Marigayi Sanata Ibrahim Mantu

 

Abuja – A ranar 17 ga watana Agustan 2021, aka wayi gari da labarin cewa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ibrahim Mantu, ya rasu.

An bada sanarwar za a yi wa Sanata Ibrahim Mantu sallah a gidansa da ke Apo, birnin Abuja.

Legit.ng Hausa ta tsakuro kadan daga cikin wannan dattijo, fitaccen ‘dan siyasa, kuma daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar hamayya ta PDP a Najeriya.

1. Yaushe aka haifi Mantu?

An haifi Ibrahim Mantu a ranar 16 ga watan Fubrairu, 1947, a kauyen Chanso, a yankin Gindiri, karamar hukumar Mangu, jahar Filato.

Rahotanni sun ce Sanata Mantu ya rasu ya na da shekara 74 bayan ya yi jinyar COVID-19.

2. Ina Mantu ya yi karatu da aiki?

Marigayin ya shiga makarantar firamare daga 1955 zuwa 1961 a Gindiri a karamar hukumar Mangu, ya samu shaidar kammala firamare a shekarar 1961.

Daga nan ya fara aiki a matsayin Kilaki a 1962 a ma’aikatar ayyuka na gwamnati a Jos.

Daga baya Mantu ya koma makarantar horas da malamai da ke Gindiri a 1964, ya kammala karatu, har ya samu takardar shaidar zama malami a 1967.

Ng News ta ce marigayin ya yi aiki da kamfanin sigarin nan, Nigerian Tobacco da ke Zariya a 1968, bayan ‘yan shekaru ya koma aiki a kamfanin UAC.

Kamar yadda shafinsa na yanar gizo ya nuna, Sanata Mantu ya karanci ilmin siyasa a jami’ar Amurka da ake kira Washington International University.

An karrama Mantu a jami’ar aikin gona ta Makurdi, jami’ar Jos, Madonna University, Okija da wata jami’a da ke birnin Port Novo, da ke kasar Benin.

3. Yadda Mantu ya fara siyasa

Sanata Mantu ta shiga siyasa a jamhuriyya ta biyu a shekarar 1978, ya zama mataimakin shugaban jam’iyyar NPN na tsohuwar jahar Filato a 1980.

A lokacin da Janar Ibrahim Babangida ya bada dama a dawo siyasa, Mantu ya nemi takarar shugabancin jam’iyyar NRC a Filato, amma bai dace ba.

Mantu ne shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaban kasan da jam’iyyar NRC ta shiga a 1993, daga baya gwamnatin soja ta soke wannan zabe.

4. Zuwansa Majalisar Tarayya a 1999

A 1998 Mantu ya zama sakataren yada labarai na jam’iyyar UNCP na kasa. Kafin Janar Abdusalam Abubakar ya soke zabuka, ya lashe kujerar Sanata.

Daga baya ya shiga jam’iyyar PDP da aka kafa, ya sake samun nasarar zama Sanatan Filato ta tsakiya. Sanata Mantu ya zarce a kan wannan kujera zuwa 2007.

5. Marigayin ya rike wasu kujeru da mukamai?

A Agustan shekarar 2001, Mantu ya zama mataimakin shugaban majalisar dattawa na kasa. Marigayin ya rike shugaban Alhazai na kasa a 2005 da 2006.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here