Cikin Kwanaki 4 ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 70 a Jahar Plateau
Kungiyar mutan Irigwe sun yi ikirarin cewa yan bindiga sun kashe musu mutum 70.
Rikici a Pleteau kwanakin baya ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiya Gwamnatin Plateau ta ce an kwantan da kuran yanzu.
Plateau – Akalla mutum 70 ne aka ce sun rasa rayukansu a garin Jebbu Miango da Kwall na karamar hukumar Bassa ta jahar Plateau sakamakon harin yan bindiga.
Kaakin kungiyar cigaba Irigwe, Davidson Malison, ya bayyana hakan ranar Alhamis yayinda yan ziyara suka ziyarci wajen da aka kai harin.
Read Also:
Ya ce an kashesu ne lokacin hare-haren da aka kwashe kwanaki hudu tun ranar Asabar zuwa Laraba ba tare da taimakon yan sanda ko wasu jami’an tsaro ba.
Malison yace an kona sama da gidaje kimanin 3000, daga ciki har da gidan tsohon dan majalisa Hon Lumumba Da’ade da kayan abinci, janareto, babura, kuma aka sace injinan ruwa.
Ya yi bayanin cewa yan bindigan Fulani Makiyaya ne suka shiga garin cikin motoci.
Yace:
“Cikin kwanaki hudu, sama da mutane 70 aka kashe, an kona gidaje 2500, an kona gonaki hekta 1000.
“Wadannan makiyayan sun kwashe dabbobi na kimanin kudi N100m. Wannan shine karo na farko da garin Irigwe zai fuskanci irin wannan hari.