‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 5 a Jahar Kaduna

 

Miyagun ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyen Madamai dake karamar hukumar Kaura ta jahar Kaduna.

An gano cewa sun tsinkayi kauyen wurin karfe 5 na asuban Lahadi inda suka dinga harbe-harbe babu kakkautawa.

Sun sheke mutum 5, 5 sun jikata yayin da suka kone gidaje 9, ababen hawa 3 duk a cikin kauyen dake jahar Kaduna.

Kaduna – A kalla mutane biyar ne suka sheka lahira yayin da wasu biyar suka jigata sakamakon farmakin da miyagu suka kai yankin Madamai dake karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna a ranar Lahadi, Daily Trust ta ruwaito.

Wani ganau ba jiyau ba wanda ya tsallake farmakin da harbin bindiga mai suna Emmanuel Nache, ya sanar da Daily Trust cewa maharan sun kutsa yankin da yawansu wurin karfe biyar na asuba kuma sun dinga harbe-harbe.

Ganau ya bada labari dalla-dalla

Yayin da naje gona da sassafe, na fara jin harbin bindiga kuma a lokacin da na fara gudu ne harsashi ya same ni a hannun dama, yace.

Nache mai shekaru hamsin da shida ya kara da cewa maharan sun tarwatsa gidaje da gonakin yankin.

Wata Linda Moses mai shekaru talatin da daya wacce ta sha da kyar, tace ta gano gawawwakin mutum hudu da ‘yan bindigan suka kashe a yankin.

An harba diyar Linda mai suna Joyce Moses mai shekaru 12 kuma ‘yar aji biyar a firamare a gabanta.Mutum biyar sun jigata kuma suna karbar taimakon likitoci a asibitin Kashim Ibrahim Yakowa dake Kafanchan.

A ina kauyen Madamai yake?

Madamai kauye ne dake karamar hukumar Kaura ta jahar Kaduna wanda ke da iyaka da Jankasa dake karamar hukumar Zangon Kataf a jahar Kaduna.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kwamishinan tsaron cikin gida, samuel Aruwan, yace an sheke mutum biyar, an kone gidaje 9, ababen hawa 3 yayin da maharan suka tsinkayi kauyen.

Wadanda suka rasa rayukansu kamar yadda Aruwan ya tabbatar sune:

Janet Yakubu, Gambk Yakubu, Jonathan Adamu, Mrs Monday da Humphrey Barnabas. Mukaddashin gwamnan jahar Kaduna, Hajiya Hadiza Sabuwa Balarabe ta roki jama’ar yankin da su kwantar da hankalinsu yayin ta umarci jami’an tsaro da su gaggauta bincikar lamarin,”Takardar ta kara da cewa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here