Yadda Yan Bindiga Suka Kashe aƙalla Mutane 30 a Jihohin Katsina da Kaduna
Hare-haren ƴan bindiga na ci gaba da salwantar da rayukan jama’a a yankin arewa maso yammacin Najeriya, musamman jihohin Katsina da Kaduna.
A ƙarshen mako an yi jana’izar mutum kusan 21 a ƙaramar hukumar Ƙankara da ke jihar Katsina, bayan wani mummunan harin yan fashin daji.
Lamarin ya kasance ne a sanadiyyar ɗauki-ba-dadi da aka samu tsakanin ɓarayin daji da ‘yan-sa-kai na tsaro a garin Majifa bayan wata walima da aka yi ta bikin ɗaya daga cikin jagororin ɓarayin wanda ake yi wa laƙabi da Mai-katifar-mutuwa a ranar Asabar a garin na yankin ƙaramar hukumar Ƙankara.
Bayanai sun ce bayan sun tashi daga walimar ne a hanyarsu ta komawa inda suka fito, ‘yan bindigar suka rika kai farmaki kan kauyukan yankin.
A wannan gari na Majifa an yi asarar rayuka da akalla sun kai kusan 20, kamar yadda bayanai suka nuna.
Wasu daga cikin mutanen yankin sun ce abu ne mai wuya a iya tantance yawan mutanen da harin ya yi sanadiyyar mutuwarsu har zuwa ranar Lahadi da daddare.
Bayanai sun nuna cewa an yi ɗauki-ba-daɗin ne a yankuna daban-daban bayan ainahin garin na Majifa inda aka fara.
Ƙauyukan da aka yi rikicin kuwa sun haɗa da Gurbi da Ɗanmarke da Gidan-Anchor da Gidan-Saika da Ɗan-mangoro da kuma Gidan-Sale.
Bayanai sun nuna cewa bayan waɗanda suka rasa ransu akwai kuma wasu mutanen aƙalla 18 da ake yi musu magani a babban asibitin Ƙanƙara.
Wani da aka harɓi ƙaninsa a ƙafa a wannan hari ya shaida wa BBC cewa, da misalin ƙarfe uku na rana ne ‘yan bindigar suka far ma yankunan nasu, inda suka riƙa harbin kan mai-uwa-da-wabi, wanda ya rutsa da yara ƙanana da mata.
Sai dai mutumin ya ce ɓarayin ba su tafi da kowa ba, amma sun kashe rayukan da ya tabbatar aka yi jana’izar mutum akalla mutum 22, waɗanda ya ce ya sani.
Kuma ya ce har yanzu mutanen yankin ba su da kwanciyar hankali saboda abin da ya faru.
Read Also:
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Katsina SP Gambo Isa wanda ya tabbatar wa da BBC wannan lamari ya ce, daman wannan yanki ne da mutanen garuruwan suke turje wa ɓarayin dajin.
Kakakin ya tabbatar da mutuwar mutane aƙalla 15 daga ɓangaren mutanen yankin da kuma mutum wajen biyar da ya ce sun ji raunuka.
Amma kuma a ɓangaren ɓarayin kakakin ya ce ba su da masaniyar yawan waɗanda aka kashe domin sun gudu da mutanensu.
Kashe-kashe a Jihar Kaduna
A jihar Kaduna wadda ke maƙwabtaka da jihar ta Katsina hukumomi sun sanya dokar taƙaita zirga-zirga a wasu sassan ƙaramar hukumar Zangon Kataf sakamakon kisan mutane da dama a garin Angwan-Wakili.
Rahotanni sun ce mutum sama da 17 aka kashe, yawancinsu mata da yara, ciki har da wata mai jego da aka yanka da jaririnta, lokacin da ‘yan bindiga suka mamayi yankin.
Mazauna yankin sun ce sun gano wasu gawarwakin a ranar Lahadi, lokacin da suka bazama neman ‘yan uwansu.
Kakakin ‘yan sanda a jihar ta Kaduna SP Mohammaed Jalige, a wata sanarwa ya ce matakin gaggawa da aka ɗauka na haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da ‘yan sa-kai na yankin, shi ne ya takaita asarar rayukan.
Amma ya ce zuwa safiyar Lahadi an gano gawar mutum goma da suka rasa ransu a hare-haren, abin da ya sa aka sanya dokar takaita zirga-zirga.
An sace wasu a Jihar Zamfara
A jihar Zamfara ma bayanai sun nuna cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutum aƙalla shida a garin Ƙauran Namoda a daren ranar Asabar.
Wasu bayanai da BBC ta samu daga wani mutumin garin sun nuna cewa masu satar mutanen sun je ne da nufin satar wasu mutum uku, kasancewar ba su same su ba sai suka yi awon-gaba da waɗannan mutum shida.
Kakakin ‘yan sanda na jihar SP Mohammaed Shehu wanda ya tabbatar wa da BBC afkuwar lamarin ya ce an tura jami’an tsaro yankin da nufin kuɓutar da waɗanda aka sace.
Kakakin ya kuma yi wa BBC ƙarin bayani kan wata nasara da ya ce sun samu inda jami’an tsaro suka kuɓutar da mutum 14 daga hannun wani fitaccen ɓarayin mutane mai suna Dogo Sule.
Mutanen da ya ce sun ƙunshi mata bakwai da maza biyu da ƙananan yara biyar sun kwashe kwana 68 a hannun ‘yan bindigar.
A bayanan nasa ya kuma ce sun yi nasarar lalata dabar ƙasurgumin ɓarawon mutanen.