‘Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Matasan Jam’iyyar APGA
Yan bindiga sun sake kai farmaki jihar Anambra inda suka kashe wani shugaban matasan jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), Emeka Alaehobi.
Miyagun sun kashe Alaehobi ne a garin Utuh da ke karamar hukumar Nnewi ta kudu a ranar Asabar, 11 ga watan Yuni.
Kakakin rundunar yan sandan jihar, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar mummunan lamarin.
Anambra – Wasu tsagerun yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe shugaban matasan jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), Emeka Alaehobi, a jihar Anambra.
An tattaro cewa an kashe Alaehobi ne a garin Utuh da ke karamar hukumar Nnewi ta kudu a ranar Asabar, 11 ga watan Yuni, kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto.
Read Also:
An tattaro cewa an sace shugaban matasan ne a ranar Alhamis, 9 ga watan Yuni, lokacin da wasu yan bindiga suka farmaki gidansa da ke garin Ukpor.
An tsinci gawarsa ne a wata mararraba da ke Utuh, yan kilomita kadan daga Ukpor, inda aka sace shi.
Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da lamarin
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa kakakin yan sandan jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa:
“Wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun rigada sun cire gawar kafin jami’anmu su isa wajen.
“Binciken da jami’anmu suka zurfafa daga wasu shaidu a yankin, ya bayyana mutumin a matsayin wani Emeka Alaehobi wanda aka sace a ranar 9/6/2022 daga gidansa da ke Ukpor, karamar hukumar Nnewi ta kudu.”
Kakakin yan sandan ya ce jami’ansu na bibiyar maharani, inda ya kara da cewa wadanda suka aikata ta’asar za su fuskanci shari’a.