‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Banga 2 a Jahar Niger

 

‘Yan bindigan daji a jahar Niger sun sheke ‘yan banga 2 a yayin wata arangama da suka yi.

Mummunan lamarin ya auku ne a yankin Mayaki da ke karamar hukumar Lapai ta jahar Niger.

Shugaban ‘yan sintirin jahar ya ce jami’ansu sun bi sahun miyagun domin damko su.

Niger – Sakamakon musayar ruwan wuta tsakanin miyagun ‘yan bindigan daji da ‘yan banga da aka yi a yankin Mayaki da ke karamar Lapai ta jahar Niger, ‘yan banga 2 sun rasa rayukansu.

Daily Trust ta rawaito cewa, Mayaki na da iyakoki da Gwaji, wani yanki na karamar hukumar Abaji da ke babban birnin tarayya.

Mazauna yankin sun ce, lamarin ya auku a ranar Lahadi wurin karfe 10:23 na safe yayin da wasu ‘yan banga suka fita sintiri kuma miyagun ‘yan bindiga suka biyo su a yankin.

Wani mazaunin yankin, wanda ya bayyana kansa da suna Ahmadu, ya ce ‘yan banga sun yi musayar ruwan wuta da miyagun inda suka sheke ‘yan banga biyu har lahira.

Ya ce daga bisani ‘yan bindigan sun tsere bayan sun gano cewa ‘yan bangan kauyen Kapako sun fara kokarin bayyana, Daily Trust ta rawaito.

Kwamandan ‘yan sintiri na jahar Niger, yankin Lapai, Muhammadu Ibrahim, ya tabbatar da mutuwar ‘yan bangan biyu.

“Tabbas mu rasa mutum biyu daga cikin jami’anmu a yayin wani sintiri da suka fita wurin dajin Mayaki,” yace.

“A yanzu da muke magana da ku, mun tura jami’anmu kuma sun fara farautar ‘yan ta’addan da suka yi aika-aikar,” ya kara da cewa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here