‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Makaranta a Kamaru

Yara shida ne suka mutu sakamakon harin da ƴan bindiga suka kai wata makaranta mai zaman kanta a yankin da ake samun tashe-tashen hankula a Kamaru, tare da jikkata wasu da dama, a cewar jami’ai.

Jami’ai a yankin kudu maso yammacin birnin Kumba sun zargi ƴan awaren yankin rainon Ingila da kai harin. Sai dai ba a iya tabbatar da hakan ba.

Wani jami’in ilimi a yankin ya ce yaran da aka kashe ɗin ƴan tsakanin shekaru 12 zuwa 14 ne.

Tun shekarar 2016 ake ta samun ƙaruwar tashe-tashen hankula a yankunan rainon Ingila na Kamaru, waɗanda ke neman a ba su ƴancin kai.

Wasu makarantun a yankunan rainon Ingila na Kamarun sun buɗe a baya-bayan nan, bayan da suka shafe shekara huɗu a rufe sakamakon barazana daga ƴan awaren da ke rikici kan samun yancin kan ƙasar Ambazoniya.

Masu fafutuka a yankin rainon Ingila sun ce yankin masu Faransanci da suka fi yawa a ƙasar sun mamaye komai tare da mayar da yankin rainon Ingila saniyar ware.

A ranar Asabar da rana ne ƴan bindiga a kan babura suka dirar wa makarantar Mother Francisca. Wasu yaran sun ji rauni a yayin da suke tsallakawa daga hawa na biyu a ƙoƙarinsu na tsere wa harin.

Bidiyon da aka ɗora a shafukan sada zumunta sun nuna yadda manya ke gudu suna fita daga makarantar ɗauke da yara.

”Sun samu yara a cikin aji sai suka buɗe musu wuta,” kamar yadda wani jami’i a birnin Ali Anougou ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Babu tabbas kan dalilin da ya sa aka kai hari makaranta, amma Mista Anougou ya ce ƴan aware ne suka kai harin.

Shugaban ƴan awaren ya ce za a fitar da sanarwar da za ta nuna rashin jin daɗi kan kashe-kashen.

Kan me ake rikicin?

A shekarar 2017 ne zanga-zangar da ake ta yi kan ci gaba da amfani da harshen Faransanci a kotuna da makarantu a yankunan Kudu maso Yammacin ƙasar da ke amfani da Turancin Ingilishi ta rikiɗe ta zama rikici.

Wani matakin tsaro da aka ɗauka ya jawo fararen hula masu amfani da Turancin Ingilishi sun ɗauki makamai don faɗa da gwamnatin Shugaba Paul Biya mai magana da Faransanci.

Dubban mutane ne suka rasa rayukansu yayin da dubun-dubata suka rabu da muhallansu a yayin da ke ci gaba da rikici tsakanin ƴan aware da dakarun tsaro.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here