‘Yan Bindiga Sun ƙona Sakatariyar ƙaramar Hukuma da Kotun Majistire a Jahar Anambra
Wasu tsagerun yan bindiga sun kone ƙaramar hukuma guda da wata Kotun Majistire a jihar Anambra da daren jiya Lahadi.
Wata majiya ta ce maharan sun kona fayil-fayin da kadarorin da ke cikin harabar wurin ciki har da motocin da aka aje.
Kakakin rundunar yan sandan jihar ya ce tuni yan sanda suka shawo kan lamarin kuma an kashe wutar baki ɗaya.
Anambra – Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun ƙona Sakatariyar ƙaramar hukumar Indemili da kuma wata Kotun Majirtire da ke cikin harabar wurin.
Wata majiya ta shaida wa Punch cewa maharan sun farmaki harabar sakatariyar ne ranar Lahadi da daddare kuma suka aikata wannan ta’adi.
Read Also:
Bayanai sun nuna cewa yan bindigan sun ƙone fayil-fayil da wasu kadarori a wurin, har da ginin Sakatariyar.
Bidiyo da hotunan harin da ke yawo a Intanet sun nuna cewa baki ɗaya Sakatariyar ta kone a harin.
Haka nan kuma, Motocin da aka aje a harabar Sakatariyar ƙaramar hukumar sun ƙone kurmus sanadin harin na daren Lahadi.
Hukumar yan sanda ta tabbatar Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin hukumar yan sanda, DSP Tochukwu Ikenga, ya alaƙanta harin da wasu masu ta da wuta da ba’a gano ba.
A kalamansa ya ce:
“Eh, tabbas lamarin ya faru kuma tuni jami’an yan sanda suka dura wurin domin dawo da komai dai-dai.”
“A halin yanzun, an kashe wutar baki ɗaya ta daina ci, kuma zaman lafiya a yankin ya dawo kamar yadda ya ke a baya.”
Wannan ba shi ne karo na farko da maharan suka ƙona sakatariyar karamar hukuma guda a jihar Anambra ba.