‘Yan Bindiga Sun Kubutar da Fursunoni Sama da 1500 Tare da Kona Motocin ‘Yan Sanda a Jahar Imo

Wasu ‘yan bindiga sun afkawa wani gidan yari da hedikwatar ‘yan sanda a jahar Imo.

An bayyana cewa, sun kubutar da fursunoni tare da kone motocin ‘yan sanda da dama.

Rundunar ‘yan sandan jahar ta tabbatar faruwar lamarin tare da shaida bincike akai.

Wasu ‘yan bindiga a safiyar ranar Litinin sun kai hari a gidan yari na Owerri da ke cikin babban birnin jahar Imo tare da kubutar da fursunoni sama da 1500.

Maharan sun kuma kone hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta jahar Imo da ke Owerri tare da kona kusan dukkanin motocin da ke ajiye a helkwatar rundunar.

‘Yan bindigar sun ci gaba da sakin wadanda ake zargin a kusan dukkanin magarkamu a sashin binciken manyan laifuka na rundunar.

Jaridar Punch ta tattaro cewa ‘yan bindigan sun fara barnar ne daga karfe 1 na dare zuwa 3 na safiyar Litinin.

Sun rera wakokin hadin kai a gidan gwamnati da ke kusa na tsawon mintuna 30 kafin su far wa cibiyoyin, in ji majiyar tsaron ga wakilin Punch.

Yayin da suka kutsa kai cikin gidan yarin tare da taimakon ababen fashewa, maharan sun ce wa fursunonin da aka tsare da su koma gidajensu.

Lokacin da aka tuntube shi, kakakin ‘yan sanda a jahar, Orlando Ikeokwu, ya tabbatar da faruwar harin.

Amma, ya tabbatar wa mutanen jahar cewa hukumomin tsaro suna bincike kan lamarin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here