Rundunar ‘Yan Sandan Jahar Neja ta Kashe ‘Yan Bindiga 3 Tare da ƙwato Bindigu 5 ƙirar AK-47

 

Hukumar ‘yan sanda a jahar Neja ta samu nasarar aika yan bindiga uku zuwa lahiya a wani musayar wuta d suka yi tsakaninsu.

A cewar yan sandan, sun sami wannan nasara ne tare da taimakon yan bijilanti da kuma wata masaniya da aka basu.

Kwamishinan ‘yan sandan jahar yace mutane su kwantar da hankalinsu, kuma sukai rahoton duk wanda suka gani da raunin harbi a jakinsa.

Rundunar yan sanda reshen jahar Neja ta ce masu garkuwa da mutane uku sun rasa rayukansu a wani bata kashi da suka yi a tsakanin su.

Yan sandan sun sami wannan nasara ne tare da haɗin guiwar jami’an sa kai (Vigilante) na garin Lapai

An kashe mutanen ne bayan samun sahihin bayanai da jami’an yan sanda suka yi cewa wasu yan bindiga sun yi awon gaba da mutane uku a wurare daban-daban.

Mai magana da yawun yan sandan jahar, DSP Wasiu Abiodun, ya ce jami’ai tare da yan bijilanti sun bi su a baya har zuwa wani daji a ƙauyen Fapo, dake ƙaramar hukumar Lapai.

Inda anan ne jami’an suka far musu akai batakashi tsakanin su, har yan sandan suka samu nasar kashe mutum uku.

Wasi’u Abiodun, ya ƙara da cewa sun kuma ƙwato bindigu guda biyu ƙirar AK-47 da kuma wata bindiga ta gargajiya guda ɗaya, Dailytrust ta ruwaito.

Ya kuma tabbatar da cewa sauran yan bindigar sun gudu da raunukan harbi a jikin su, sannan kuma an kuɓutar da mutane ukun da suka sace.

Hakanan kuma, kwamishinan ‘yan sandan jahar, Adamu Usman, ya yi kiɗa ga al’umma da su kwantar da hankalinsu, jami’ai zasu cigaba da yaƙar duk wani wanda baya buƙatar zaman lafiya.

Ya kuma roƙi mutanen jahar Neja da su kai rahoton duk wanda suka gani da raunin harbi a jikinsa ga ofishin yan sanda mafi kusa da su.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here