ƴan Bindiga Daga Mali Sun Kashe Mutane 17 a Sokoto

 

Hukumomi a jihar Sakkwato da ke arewacin Najeriya sun ce wasu ƴan bindiga daga Mali da suka tsallako iyaka daga Nijar sun kashe mutane kimanin 17 ciki har da jami’an sabuwar rundunar tsaro da gwamnatin jihar ta Kafa su biyar.

Kashe-kashen dai sun faru a ƙaramar Hukumar Gudu mai iyaka da jamhuriyar Nijar.

Kantoman ƙaramar hukumar ta Gudu, Umar Maikano Ballee ya shaida wa BBC cewa hare-haren na ‘yan bindigar da ake kira lakurawa sun fara ne daga ranar Asabar.

A cewarsa sun kai hari biyu – garin ƙarfen China inda suka harbi manoma shida har guda huɗu suka mutu nan take sai biyu da ke jinya a asibiti, guda a cikinsu rai ya yi halinsa ranar Talata.

“Bayan kwana ɗaya suka sake zuwa ƙarfen sarki suka kashe mutum takwas, cikinsu akwai jami’an tsaron alumma, da sauran mutanen gari huɗu.” in ji shi.

Kantoman ya ƙara da cewa suna zargin lakurawa masu shigowa daga Mali da kai hare-haren biyu.

“Sun shigo yankin ranar Alhamis da ƙarfe shida na yamma, sun shigo ta gefen jimajimi, daga nan suka zo suka tsallaka wannan titin na kurdula suka tsallaka nan garin Jeji suka tsallaka kokotau suka tsallaka wannan dajin na ƙarfen sarki.” kamar yadda ya bayyana.

Ya ce ba shi da masaniya kan abin da ya haɗa lakurawan da mutanen garuruwan sai dai ya ce “abin da muka sani sun zo waɗan nan ƙauyuka suna kora shanun mutane, a kwana na biyu sai suka shiga suna harbin manoma.”

Balle ya ce akwai jami’an tsaro da ke kare jama’a sai dai a ranar da lamarin ya faru, an yi ruwan sama, abin da ya kawo cikas ga jami’an tsaron su kai ga ƙauyukan a motocinsu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here