‘Yan Bindiga Sun Sace Daliban Makarantar Islamiyya a Jahar Katsina

 

‘Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari Islamiyya a karamar hukumar Faskari, jahar Katsina.

‘Yan bindigan sun sace dalibai da dama sannan sun yi awon gaba da malamin makarantar islamiyya guda daya.

Rundunar yan sandan jahar Katsina ta bakin kakakinta SP Gamba Isah ta ce ba za ta iya tabbatar da harin ba a yanzu.

Faskari, Jahar Katsina – Yan bindiga sun sace dalibai da dama da malami guda daya a makarantar Islamiyya da ke kauyen Sakkai a karamar hukumar Faskari ta jahar Katsina, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar rahoton na Daily Trust, an sace daliban ne yayin da suke daukan darrusa a harabar makarantar da yamma.

A halin yanzu ba a kammala tattaro bayannan yadda lamarin ya faru ba.

Ba a san inda aka tafi da wadanda aka sace din ba a lokacin hada wannan rahoton.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here