Gwamnatin Gombe ta Kashe Sama da N100m Wurin Daukar Nauyin Mahajjata Kiristoti 70 – Karu Ishaya

 

Karu Ishaya, sakataren hukumar walwalar mahajjata kiristoci na jahar Gombe, ya ce gwamnatin jahar ta kashe fiye da naira miliyan 100 wurin tallafawa mahajjata.

Ishaya ya bayyana hakan ne a otal din Dead Sea Spa dake Sweimeh dake Jordan yayin amsa tambayoyin manema labarai.

A cewarsa, cikin kudaden da gwamnati ta narka har da kudaden da aka yi amfani dasu wurin yi wa mahajjatan guda 70 gwajin cutar COVID-19.

Gombe – Karu Ishaya, sakataren hukumar samar wa da mahajjatan addinin kirista walwala, CPWB, na jahar Gombe ya bayyana yadda gwamnatin jahar Gombe ta kashe fiye da naira miliyan 100 wurin daukar nauyin mahajjatan kiristoci 70 zuwa kasar Jordan.

Gwamnati ta tallafawa mahajjata

A cewarsa irin karamcin da gwamnatin jahar ta nunawa masu bautar ya sa su matukar farin ciki.

A cewarsa an yi amfani da wani bangare na kudin wurin yi wa mahajjatan gwajin cutar COVID-19, Daily Nigerian ta wallafa. Ya ce gwamnatin jihar tayi duk wani kokari na ganin ta biya kudin gwajin cutar COVID-19 ga mahajjatan har da wadanda suka biya wa kansu hajjin.

Gwamnatin jahar tana nuna kwadayinta kwarai akan harkokin addinai.
Game da kokarin da gwamnatin jahar Gombe tayi, ina bukatar mutane su mika godiyarsu gare ta duk da halin tsananin rayuwar da ake ciki a halin yanzu.

Idan aka duba yadda gwamnatin jahar Gombe ta kashe fiye da naira miliyan 100 duk don taimakawa addinin Allah, dole a godewa gwamna Inuwa Yahaya bisa yi mana hidimar akan abinda ya kawomu Jordan, a cewar Ishaya.

Hajji yana karawa jama’a Imani

A cewarsa, hajji yana kara wa mabiya addini imani musamman kaje ka hani kuma ka koma ka cigaba da aiwatar da abubuwan da ka gani ta hanyar yin wa’azi da ya da soyayya.

Ya bukaci mahajjatan da su dauki damarar samar da hadin kai idan sun koma gidajensu.

A matsayinmu na kiristoci a jahar Gombe, ya kamata mu cire kabilanci mu rungumi kowa a matsayin ‘yan uwan da babu wanda ya isa ya raba mu.

Dangane da cutar COVID-19, Ishaya ya ce babu wani abin fargaba don yanzu haka mutum daya kacal aka samu da cutar kuma yanzu haka an killace shi ana kulawa da lafiyarsa.

A cewarsa, an gwada duk sauran mahajjatan har sau biyu kumu duk babu wanda yake dauke da cutar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here