‘Yan Bindiga Sun Sace ɗan Tsohon Sakataren Kungiyar Likitoci ta Kasa, Dr. Adewunmi Alayaki
Wasu yan bindiga da ba’a san ko suwaye ba sun yi awon gaba da ɗan tsohon sakataren kungiyar NMA.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun sace Adedamola Alayaki, a gonar mahaifinsa ranar Laraba.
Hukumar yan sanda reshen jahar Ogun ta tabbatar da faruwar lamarin, tace a halin yanzun jami’anta sun fara bincike.
Ogun – Yan bindiga sun sace ɗan tsohon sakataren kungiyar likitoci ta kasa (NMA), Dr. Adewunmi Alayaki, a jahar Ogun, kamar yadda Punch ta rawaito.
Yan bindigan da suka sace ɗan sakataren, Adedamola Alayaki, sun nemi a tattara musu kuɗin fansa miliyan N20m kafin su sake shi.
Read Also:
Legit.ng Hausa ta tattaro muku cewa an yi awon gaba da ɗan tsohon sakataren ne a gidan gonar mahaifinsa dake yankin Isaga-Orile, karamar hukumar Abeokuta ta arewa, jahar Ogun.
Yan sanda sun kaddamar da bincike
Kakakin rundunar yan sanda reshen jahar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin ga mannema labarai ranar Alhamis.
A bayanin Oyeyemi, Adedamola shine shugaban ɗaya daga cikin gidan gonan mahaifinsa.
Kakakin yan sandan ya tabbatar wa manema labarai cewa jami’an hukumar yan sanda na kan gudanar da bincike don kamo masu garkuwan.
Yace:
“Mun matsa sosai kan lamarin, kuma jami’an mu na kan bincike don gano waɗanda suka sace shi.”
Channels tv ta rawaito cewa lamarin satar mutane domin neman kuɗin fansa ya zama ruwan dare a wasu sassan Najeriya.
Sai dai wannan sace ɗan tsohon sakataren NMA da ya faru ranar Laraba shine na baya-bayan nan a jahohin kudu maso yammacin kasar nan.