‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane 7 a Unguwar Zango Dake Jahar Kaduna

 

‘Yan bindiga sun afka unguwar Zango da ke Samarun Zaria a jahar Kaduna sun sace a kalla mutane bakwai.

Wani shaidan gani da ido ya ce maharan sun afka unguwar ne da tsakar dare a lokacin mutane suna barci.

Ya ce sun rika shiga gidaje da tsakar daren sannan sun shafe kimamin mintuna 30 suna ta harbe-harbe kafin suka tafi.

Zaria, Jahar Kaduna – A kalla mutane bakwai ne wasu yan bindiga suka sace yayin da suka kai hari a unguwar Zango a Samarun Zaria da ke jahar Kaduna, The Cable ta rawaito.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigan sun afkawa unguwar ne ta hanyoyin shiga daban-daban misalin karfe dayan daren Juma’a a yayin da mutane ke barci.

Wani shaida ya ce:

“Yan bindigan sun kai hari wasu gidaje a yankin a yayin da suke ta harbe-harben bindiga na tsawon mintuna 30.

“Dan uwa na ya fara kira na a waya, yana cewa masu garkuwa da mutane sun shigo Zango, daga nan na fara jin karar harbin bindiga a gaban gidanmu. Nan take na tafi na duba ‘ya’ya na na gano suna barci.”

“Na leka ta tagar; domin ina tunanin sun riga sun shigo gidan mu ne. Sun buga kofar gidan mu sau uku sannan suka sha ruwa a famfon da ke kofar gidan a waje.

“Duk wanda ka kira sai ya ce maka sun wuce ta kofar gidansu. Kawo yanzu an fada masa mutum bakwai aka sace. Abin da muka sani kenan yanzu. Sun shiga gidaje da yawa. Ina da tabbacin sun sace fiye da hakan.”

Kakakin yan sandan jahar Kaduna, Mohammed Jalige bai daga wayarsa ba kuma bai amsa sakon kar ta kwana ba a lokacin hada wannan rahoton.

A baya-bayan nan dai yan bindiga suna yawan kai hare-hare a sassan jahar Kaduna.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here