‘Yan Bindiga Sun Sako Daliban Kwalejin Noma ta Jahar Zamfara Dake Bakura
Rahoto daga jahar Zamfara na tabbatar da cewa, an sako daliban da aka sace a kwalejin noma ta Bakura.
An rawaito cewa, gobe Juma’a za a kai daliban da malamansu da aka sako zuwa fadar gwamnatin jahar.
An sace daliban ne kwanakin baya, lamarin da ya kai ga dakatar da zaman majalisar dokokin jahar.
Zamfara – An sako malaman makaranta da daliban kwalejin aikin gona da kimiyyar dabbobi ta jahar Zamfara dake Bakura.
Read Also:
Wata majiya daga tushe na kusa da gwamnatin jahar Zamfara da ta nemi a sakaya sunanta ta sanar wa jaridar Punch cewa za a kawo su gidan gwamnati gobe Juma’a 27 ga watan Agusta, amma, ya ki yin karin bayani.
Idan za a iya tunawa a ranar 16 ga watan Agusta, 2021 wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai hari kwalejin tare da sace mutane 19 da suka hada da ma’aikata uku, dalibai 15 da direba.
An kashe mutane hudu yayin da ‘yan bindigan suka yi awon gaba da dalibai da malamai na makarantar.
An tattaro cewa yan bindigan sun kai hari kwalejin aikin gona ta Zamfara dake karamar hukumar Bakura a ranar Lahadi lokacin da lamarin ya faru.
Mataimakin magatakardar kwalejin, Atiku Aliyu Bakura, ya tabbatar da sace mutanen. An ruwaito Bakura yana cewa mutane hudu da suka hada da dan sanda da masu gadi uku sun mutu a harin.