Matsalar Tsaro: Sanata Ali Ndume Ya Nuna Damuwarsa Kan Shirun Shugaba Buhari

 

Sanata Ali Ndume, ya kirayi shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya fito ya yiwa yan Najeriya jawabi.

Sanatan APC yace bai kamata Buhari ya yi gum da bakinsa a lokacin da matsalar tsaro ke kara ta’azzara ba.

Sai dai sanatan ba shi da shilafa cewa sojoji zasu zakulo waɗanda suka kai musu hari NDA ko ina suka ɓuya.

Abuja – Shugaban kwamitin sojojin ƙasa, Sanata Ali Ndume, ya nuna matukar damuwarsa kan shirun shugaba Buhari game karuwar matsalar tsaro a faɗin kasa, kamar yadda dailytrust ta rawaito.

Ndume, wanda ke wakiltar mazabar Borno ta kudu a majalisar dattijai, ya roki Buhari ya daina magana ta bakin mataimakansa a kan muhimmin abu kamar tsaron kasa.

Sanatan ya yi wannan furuci ne a wata hira da yan jarida a Abuja yayin da yake tsokaci kan harin da yan bindiga suka kai NDA.

“Ina damuwa sosai da rashin jawabin shugaban ƙasa ga yan Najeriya. Shiru a halin da ake ciki ba abu ne mai kyau ba.”

“Idan har shugaban Amurka zai dinga jawabi kullum saboda abinda ke faruwa a kasar Afghanistan, Zan tsammaci shugaban ƙasa zai wa yan Najeriya jawabi kullum ko mako-mako ko duk bayan mako biyu kan halin da ake ciki a faɗin kasa.”

“Kalaman da mataimakan shi suke yi ba mafita bace, ya kamata shugaban kasa ya samu wani lokaci da zai rinka yiwa yan kasa bayanin halin da ake ciki da kuma matakin da gwamnati ke ɗauka.”

Wane tasirin bayanin Shugaba zai wa yan Najeriya?

Ndume yace jawabin shugaban ƙasa ka iya rage radaɗin damuwa da tsoron dake cikin zukatan yan Najeriya idan suka ji matakan da ake ɗauka.

Sanatan yace ya kamata shugaban ya rinka ziyartar inda wani abu ya faru domin gane wa idonsa yanayin da ake ciki.

Ku zakulo bara gurbin cikinku

Sanata Ndume ya bayyana tabbacin cewa sojoji zasu zakulo gungun yan bindigan da suka kai hari makarantar sojoji NDA.

Sai dai ya roki jami’an sojojin su fallasa bara gurbin dake cikinsu, waɗanda ke baiwa yan ta’adda bayanai.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here