Yanda ‘Yan Bindiga Suka Salwanta Rayukan Jama’a
Masu garkuwa da mutane suna cigaba da kai hare-hare kauyakun jihar Kaduna.
‘Yan ta’addan sun kai hari Kajuru, Igabi, Giwa da Zangon Kataf ranar Litinin da Talata.
Sakamakon hare-haren, mutane 16 sun rasa rayukansu, sun kuma yi garkuwa da wasu.
‘Yan bindiga sun cigaba da kai hare-hare kananun hukumomi da ke karkashin jihar Kaduna, kamar Kajuru, Igabi, Giwa da Zangon Kataf, inda suka kashe a kalla mutane 16 a ranar Litinin da Talata.
Sun saci mutane da dama, kuma sun harbi a kalla mutane 4.
Read Also:
Sun kai hari a ranar Lahadi hanyar Kaduna zuwa Abuja har suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 15, kuma suka kwashe daliban jami’ar Ahmadu Bello 8.
Gwamnatin jihar Kaduna, ta tabbatar da kisan mutane 11 a kauyen Albasu, da ke karkashin karamar hukumar Igabi, Daily trust ta ruwaito.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya ce wasu mutane 4 sun rasa rayukansu sakamakon raunukan da ‘yan ta’addan su ka ji musu.
Jami’an tsaro sun ce an kashe wani Albarka Addu’a, tsohon dagacin kauyen Kyemara Gari a ranar Lahadi, bayan ‘yan bindigan sun yi garkuwa da wasu mutane 2 a Maraban Kajuru a karamar hukumar Kajuru.
Ya kuma tabbatar da harin da aka kai kauyakun Fatika, Kaya da Yakawada da ke karkashin karamar hukumar Giwa a ranar Talata, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutane 2, sannan an yi garkuwa da mutane da dama.