Mazauna Karkara na Babban Birnin Tarayya Sun Koka Kan ‘Yan Bindiga na Kafa Sansani a Yankunan su

 

Yayin da hare-haren bama-bamai na sojoji ke ci gaba da faruwa a jahohin arewacin kasar, rahotanni na cewa ‘yan bindiga da ke tserewa suna kafa sansanoni a birnin tarayya.

Mazauna kauyukan da ke garuruwan sun tabbatar da cewa sun gamu da ‘yan bindigar sau da yawa.

Sai dai kuma kakakin ‘yan sandan birnin tarayya, DSP Adeh Josephine, ta yi alkawarin yin bincike a kan lamarin.

Akwai fargaba a wasu yankunan karkara na Babban Birnin Tarayya (FCT) biyo bayan rahotannin da ke cewa ‘yan bindiga da ke tserewa daga Arewa suna kafa sansani a dazuzzukan yankin.

Jaridar Daily Trust ta tattaro daga wasu mazauna yankin cewa barayin sun kafa sansani a kewayen Zukpatu, Gadoro, Achimbi, Pesu, Duda, Pani, Gaube da New Gwombe a karamar hukumar Kuje.

Yawancin garuruwan suna raba iyaka da Jahar Nasarawa.

Jaridar ta kuma rawaito cewa yankin Kuje na da garuruwa sama da 400 da ba su da wata hanyar sadarwa.

An kuma tattaro cewa yan fashin suna amfani da damar yawan tsaunuka a yankunan wajen kafa sansanonin su.

Wasu mutanen kauyukan, wadanda aka zanta da su, sun bayyana cewa duk da cewar ‘yan fashin ba su fara kai musu farmaki ba, amma suna gargadin su da kada su tona asirin maboyar su ga jami’an tsaro.

Wani mazaunin Gaube, wanda ya bayyana sunansa da Ibrahim, ya ce kafa sansanin da ‘yan fashin suka yi ya haifar da fargaba.

Ya kara da cewa mazauna yankunan, musamman manoma, yanzu suna zuwa gonakinsu cikin tsoro.

Ibrahim ya ce:

“A duk lokacin da ‘yan fashin suka ci karo da mazauna garuruwan a gona ko rafi, kawai suna gargadin mu da kada mu kai rahoton wuraren da suke ga jami’an tsaro.”

Ya kara da cewa a wasu lokutan ‘yan fashin suna baiwa mazauna yankin kudi don saya musu kayan abinci da sauran abubuwa.

Wani wanda aka yi garkuwa da shi a yankin Pegi na Kuje, wanda ya nemi a sakaya sunansa, yayin da yake korafin halin da ya tsinci kansa a hannun ‘yan bindigar, ya ce sun kafa sansani a saman tsaunuka.

Ya ce:

“Akwai bukatar gwamnati ta yi wani abu cikin gaggawa kafin lamarin ya kara muni saboda abin da na gani. Ina mamakin yadda waɗannan masu laifi suka sami damar isa ga irin waɗannan wuraren da makamai.”

Wani mazaunin garin Gwombe wanda ya bayyana sunansa da Alhassan ya ce ‘yan bindiga sun mamaye dajin da ke kewayen garin.

Alhassan ya ce:

“Ina ganin tun da suka kai hari tare da yin garkuwa da wasu mutane a kauyen mu a farkon wannan shekarar, ba su sake kai wa mutanen mu hari ba, sai dai su aiki mutanen mu da suka ci karo da su a kan hanya sannan su gargade su kan fadawa jami’an tsaro maboyar su.”

Wani basarake a birnin na tarayya wanda ya fi son a sakaya sunansa, ya ce kafa sansanin ‘yan bindiga a wasu dazuzzuka a yankunan karkara na matukar barazana ga rayuka da dukiyoyin jama’a.

Ya tuno da yadda ‘yan bindiga suka kai hari kan matafiya da mutanen gari a kan hanyar Gaube zuwa Kuje a bara, wanda ya sanar da kafa rundunar hadin gwiwa a kewayen al’umma.

Ya ce:

“Amma a yau, rundunar tsaro ta bar yankin kuma masu garkuwa da mutanen sun dawo, suna dibar mutane a kusa da yankin Gaube.”

Basaraken ya ci gaba da cewa mafarauta da manoma galibi suna cin karo da ‘yan fashin amma suna tsoron fallasa su.

Don haka, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta hanzarta daukar mataki, tare da hada kai da sarakunan gargajiya domin magance matsalar rashin tsaro a yankin.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, DSP Adeh Josephine, ta nemi a ba ta lokaci don yin bincike kan lamarin kamar yadda jaridar ta rawaito.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here