Adadin Gidajen da ‘Yan Bindiga Suka Shiga a Harin NDA

 

‘Yan bindigan da suka shiga barikin Afaka da ke NDA a jahar Kaduna ranar Talata sun afka gidaje 5 wadanda suke kusa da juna ne.

Kamar yadda jami’an binciken sirri suka tabbatar, sun ci karensu babu babbaka ne saboda dakarun sojoji basu yi saurin zabura ba.

Sannan sun yi hanzarin yin ta’addancinsu cikin gaggawa sannan suka lallaba suka tsere cikin dan kankanin lokaci.

Kaduna – ‘Yan bindigan da suka shiga barikin Afaka da ke NDA a jahar Kaduna ranar Talata sun fada wa gidaje 5 da ke makwabtaka da juna ne.

An samu wannan bayanin ne a wata takarda wacce Daily Trust ta gani.

Kamar yadda jami’an binciken sirri suka bayyana, ‘yan bindigan sun ci karensu babu babbaka saboda sojojin ba su yi gaggawar zabura ba a kan lokaci.

Lokaci mai tsawo da sojoji suka dauka a ranar da aka kai harin shi ya bai wa ‘yan bindigar damar balle har gidaje 5 da ke makwabtaka da juna sannan suka yi gaggawar tsere wa kafin sojojin su motsa,” kamar yadda takardar tazo.

Daily Trust ta rawaito cewa, take a wurin suka harbe manyan sojoji har lahira sannan suka yi garkuwa da wani manjo.

Akwai wani soja da ya samu miyagun raunika, yana asibiti ana kulawa da lafiyarsa a asibiti.

Janar Lucky Irabor ya kai ziyara wurin da lamarin ya faru, kuma ya ce lamarin ya fi kama da hauka.

Lamarin da ya faru a Kaduna ya fi kama da fashi da makami. Abin bai yi kama da ta’addanci zalla ba,” a cewarsa.

Kada wani ya damu da matsalar rashin tsaro. Shiyasa zamu yi gaggawar ganin mun kawo karshen irin wannan haukar.”

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here