‘Yan Bindiga Sun Shiga Jami’ar Jahar Taraba Sunyi Garkuwa da Lakcara 1
Wasu yan bindiga sun kutsa kai gidajen kwanan malaman jami’ar jahar Taraba, inda suka sace wani lakcara.
Shugaban Makarantar (VC), Farfesa Ado-Tenebe ya tabbatar da faruwar lamarin, yace yayi matuƙar mamaki yadda akai haka ta faru a jami’arsa.
Ya ƙara da cewa zasu cigaba da ɗaukar matakan duk da ya kamata domin ganin an magance faruwar irin haka nan gaba.
Wasu yan bindiga sun kutsa kai cikin jami’a sun yi awon gaba da malami a gidajen kwanan malamai a jami’ar jahar Taraba dake Jalingo, babban birnin jahar, kamar yadda channels tv ta ruwaito.
Lakcaran mai suna, Umar Buba, shugaban sashin koyar da ilimin gandun daji, an sace shi ne da safiyar Lahadi a cewar shugaban jami’ar, farfesa Vincent Ado-Tenebe.
Read Also:
Ado-Tenebe, wanda ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, yace maharan sun yi harbi a sama domin tsoratar da jami’an tsaron dake gadi a wajen.
Yace: “Wannan labari ne mara daɗi, kuma bai taɓa faruwa ba shekaru 2-3 da suka wuce, tun sanda aka ɗauke daraktan yaɗa labarai.”
“Nayi matuƙar mamaki da haka ta sake faruwa a jami’ar mu sabida matakan da muka ɗauka tun bayan faruwar wancan lamarin. Nasan muna da jami’an yan sanda, jami’an NSCDC, da jami’an sa kai da muka ɗauka domin su kare mu daga irin wannan harin.”
Shugaban makarantar ya bada tabbacin za’a yi iya bakin ƙoƙarin da ya kamata wajen ganin an ƙaro jami’an tsaro, da kuma buƙatar kayan aiki ga jami’an domin yaƙar yan ta’addan.
Yace ma’aikatan makarantar da ɗalibai ba zasu iya tunkarar yan bindiga da hannun su ba, ya ƙara da cewa hukumar makarantar zata duba yuwuwar yadda za’ayi ma’aikata su mallaki bindiga bisa doka domin kare kan su.