‘Yan Bindiga na Taruwa a Dajin Falgore Duk da Jahar na Kokarin Bude Dajin – Gwamna Ganduje
Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan Kano ya koka kan yadda yan bindiga ke mamaye dazukan jaharsa.
Ganduje ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kaiwa sabon shugaban sojoji Manjo Janar Farouk Yahaya.
Gwamna Ganduje ya roki rundunar ta sojoji ta yi gaggawan cigaba da aikin da ta fara a dajin Falgore na gina sansanin bada horaswa.
Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa yan bindiga sun fara mamaye dazukan jaharsa kuma akwai yiwuwar suna shirin kai hare-hare ne, Tha Nation ta ruwaito.
The Punch ta ruwaito cewa gwamnan ya yi wannan furucin ne a Hedkwatar Tsaro inda ya gana da shugabannin sojoji, ya ce yan bindigan na taruwa a dajin Falgore duk da jahar na kokarin bude dazukan.
Read Also:
Duk da cewa ya bada tabbacin gwamnatinsa da hukumomin tsaro za su cigaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya a jahar, gwamnan yayin ganawa da babban hafsan sojojin kasa, Manjo Janar Farouk Yahaya, ya roki sojojin su yi gaggawar aikin kafa sansanin horas da sojoji a dajin Falgore don sojoji su karbe dajin.
Ganduje ya ce zaman lafiyar da ake samu a jaharsa ta samu ne bisa kyakyawar alaka da ke tsakanin gwamnatinsa da hukumomin tsaro.
A cewarsa, “Na kawo ziyara ne don jajantawa sojoji bisa rasuwar tsohon shugaban hafsin sojojin kasa Laftanat Janar Ibrahim Attahiru da wasu jami’ai 10.
Abu ne mai ciwo amma munyi tawakkali duba da cewa sun rasu ne yayin yi wa kasarsu hidima.
Na kuma zo nan ne don neman taimakon Rundunar Sojojin Nigeria wurin tabbatar da zaman lafiya a jahar Kano; yan bindiga sun mayar da wasu dazukan jahar mabuyarsu.
“Muna gina gidaje, makarantu da asibitoci domin makiyaya a wasu dazukan amma duk da haka muna son sojoji su fara aiki a dajin Falgore.”
A jawabinsa, babban hafsan sojojin na kasa, ya yi alkawarin zai ziyarci Falgore domin ganin yadda za a cigaba da ayyukan sojoji a dajin.
Ya ce rundunar sojoji da sauran hukumomin tsaro za su cigaba da ganin sun dakile kallubalen tsaro a kasar.