‘Yan Bindiga Sun yi Watsi da Damar da Suka Samu ta Sulhu a Baya – Gwamna Matawalle

 

Gwamnan jahar zamfara da ke arewacin najeriya, bello matawalle ya ce ‘yan bindiga sun yi watsi da damar da suka samu ta sulhu a baya, yanzu tsakanin gwamnati da su sai aikawa lahira.

Cikin wani bidiyo da ke ta yawo a kafafen sada zumunta, an ga Gwamna Matawalle yana jawabi a wani masallaci bayan idar da sallah, inda yake yi wa al’umma bayani kan halin da ake ciki a jahar.

Matawalle ya ce “gaskiyar magana suna shan wuta sosai, ko jiya an turo kwamiti babba a sameni, cewa in tsagaita don Allah, in saki a rika samun abinci na ce wallahi ba zan saki ba,”.

“Duk wani abu da Allah ya ce muyi munyi, saboda haka mun yi iyakar yinmu, yanzu abin da muke yi shi ne mu sada su da ubangijinsu su amsa tambayoyi ga Allah.”

A watan Fabirairu, Gwamnan ya ce sulhu da ‘yan bindigar ne zabi na karshe da ya rage domin shawo kan matsalar tsaro a Najeriya.

Amma a yanzu Gwamnan ya ce matakin yakarsu ba dare ba rana suka dauka domin sun ki amfani da damar da aka ba su.

Ya rarrashi mutanen jahar da su yi hakuri game da datse layukan waya da aka yi a fadin jahar, an yi ne domin samar da zaman lafiya mai dorewa ga al’ummar jahar Zamfara.

Matawalle ya ce in Allah ya yarda Zamfara za ta samu lafiya, don haka a shirye yake ya sha walaha tare da mutanen jahar domin a gudu tare a tsira tare.

“Idan aka daina shigar da abinci da itace da man fetur da kuma amfani da babura ‘yan bindigar za su fito su rika mika kansu da kansu.

“Yan siyasa su ji tsoron Allah su daina sayan babura suna raba wa mutane, wadanda su kuma daga baya suke sayar wa wadannan miyagu.” in ji Matawalle.

Gwamnan ya ce yanzu ‘yan bindigar na tserewa zuwa wasu jahohi da ke makwabtaka domin wuyar da suke sha a jahar Zamfara.

Wuya ce ta dan lokaci da idan aka jure mata za ta samar da kwanciyar hankali a cewarsa.

Jahar zamfara na daya daga cikin jahohin da ke fama da ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a Najeriya.

Wannan ne ya sanya gwamnatin jahar ta dauki wasu matakan dakile wannan matsala, ta hanyar hana fitar da dabbobi daga jahar baki daya.

Gwamnan jahar ya ba da umarnin rufe duka kasuwannin da ke ci mako-mako a jahar, ya yin da za a rika yin bincike mai tsauri kan kayan abincin da ake safararsu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here