‘Yan Bindigan Jahar Zamfara Sun Shirya Mika Wuyansu – Gwamnan Matawalle

 

Bello Mohammed Matawalle ya kare matsayar Gwamnatin jahar Zamfara.

Gwamna ya ce mutanen Jihar sun ga amfanin yin sulhu da ‘yan bindiga.

Matawalle yayi albishir da shirin mika wuyan wasu fitinannun tsagerun.

Gwamna Bello Mohammed Matawalle na jahar Zamfara, ya ce an kammala tattauna wa da ‘dan shugaban ‘yan bindigan da aka kashe, Buharin Daji.

Daily Trust ta rahoto gwamnan ya na cewa yaron Buharin Daji, mahaifiyarsa da wani babban jagoran ‘yan bindiga a Zamfara za su ajiye makamai.

Jaridar ta ce gwamnan na Zamfara ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya zauna da tawagar shehin malamin nan na Kaduna, Ahmad Abubakar Gumi.

Ahmad Gumi ya ziyarci sansanin ‘yan bindiga a Zamfara, inda ya lallabesu, su ajiye kayan fada.

Mai girma gwamnan ya ce matakin da ‘yan bindigan su ke shirin dauka na ajiye makaman yaki zai yi sanadiyyar samar da zaman lafiya a jahar Zamfara.

Bello Mohammed Matawalle ya ce ba don jajircewarsa ba, da ya yi watsi da sulhun da aka ayi da ‘yan bindiga, saboda akasin ra’ayin da wasu su ke da shi.

“Ana ta matsa mani lamba daga wurare da-dama saboda na yi sulhu da ‘yan bindiga, wasu sun ce ina cikinsu, wasu sun ce ina ba su kariya.” Inji Gwamnan.

Mun ga tasirin kwarai na wannan yarjejeniyar (sulhu). Kasuwannin kauyuka su na dawowa. Mun ceto mutanen da aka tsare ba tare da harbin ‘dan kowa ba.”

“Idan mun san za a iya kawo karshen rikicin da karfin bindiga, da ba zamu yi sulhu ba. Za kuma mu cigaba da yin haka, duk da abin da mutane za su ce.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here