‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Karamar Hukumar Magama Dake Jahar Neja
Miyagun ‘Yan bindiga sun kuma aukawa wani Kauye a cikin jahar Neja.
Wannan karo an hallaka mutane bakwai a karamar hukumar Magama .
‘Yan bindigan sun dura garin Yangalu dauke da makamai a kan babura.
Mutane bakwai ake zargin sun mutu yayin da wasu ‘yan bindiga su ka kai hari a kauyen Yangalu, karamar hukumar Magama da ke jahar Neja.
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa ‘yan bindiga birjik su ka auka wa mutanen Yangalu, inda su ka rika buda wuta, suna harbi ta ko ina.
Kamar yadda mu samu labari dazu, wadannan miyagu da su ka zo dauke da bindiga sun tada hankalin jama’a da suka shiga harba bindigogi.
Read Also:
A ‘yan kwanakin nan, irin wadannan munanan hare-hare suna neman zama ruwan dare a jahar Neja.
‘Yan bindigan sun goya junansu a kan babura, suna rike da bindigogi.
A haka suka shiga kauyen, su ka yi barnarsu, ba tare da an kawo wani dauki ba.
Rahotanni sun bayyana a halin yanzu, ‘yan bindiga sun yi ta’adi a kauyuka kusan 70. Hakan ya jikkata Bayin Allah da-dama, sannan an kashe wasu.
Kafin ‘yan bindigan su fita daga kauyen Yangalu, sai da suka tabbata sun yi wa al’umma barna, suka jawo wa mutane asara, aka zubar da kayan abinci.
Shugaban karamar hukumar Magama, Alhaji Sufiyanu Yahaya, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari, kuma har ya taka kafarsa ya ziyarci kauyen.
Da ya je yi wa al’ummar Yangalu jaje, Sufiyanu Yahaya, ya sha alwashin cewa gwamnati za ta yi duk abin da ya dace domin a inganta tsaron yankin.