Ka Fito ka Dinga yi wa ‘Yan Najeriya Magana Tunda ba Garba Shehu da Adesine Muka Zaba ba – Melaye ga Shugaba Buhari

 

Tsohon sanata da ya taba wakiltar mazabar Kogi ta yamma, Dino Melaye yace ‘yan Najeriya Buhari suka zaba.

Melaye ya bukaci Buhari da ya bude baki ya dinga yi wa ‘yan Najeriya magana tunda ba Garba Shehu da Adesina suka zaba ba.

A cewarsa, matsalar tsaro na da nasaba da gazawar shugaban kasan, don haka yake kira gareshi da ya yayi murabus.

Dino Melaye, tsohon sanatan da ya taba wakiltar Kogi ta yamma, yace shugaban kasa Muhammadu ko yaushe baya nan kuma bashi da lokaci. Jigon jam’iyyar PDP yace ba zai yuwu shugaban kasan ya ki yi wa kowa magana ba sai ta bakin masu magana da yawunsa, TheCable ta wallafa.

Ya ce shirun Buhari na da matukar illa ga yaki da rashin tsaro a kasar nan. Melaye ya sanar da hakan ne a yayin tattaunawar da aka yi da shi a AIT ranar Juma’a.

“Akwai bukatar shugaban kasa yayi magana kai tsaye da ‘yan Najeriya, akwai bukatar yayi magana da kafafen yada labarai.

Tamkar babu shugaban kasa kuma hakan yana da matukar illa ga yaki da ta’addanci a kasar nan,” yace.

“Abun takaici ne. Babu abinda muke ji illa fadar shugaban kasa tace kaza da kaza.

Ba mu zabi Garba Shehu da Adesina ba. “Dukkan matsalar tsaronmu tana da tushe ne da rashin shugabanci nagari.

Shugaban kasar Najeriya ya gaza, ba zai iya ba. Abinda nake tsammanin daga gareshi tunda ya nuna dukkan alamun gazawa na mulkin kasar nan.

“Shugaban kasa Buhari yayi murabus saboda ‘yan Najeriya na mutuwa babu wani dalili.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here