Bayan Gyara: ‘Yan Boko Haram Sun Kara Lalata Wutar Lantarkin Maiduguri
Kimanin awanni 48 bayan gyara wutan birnin Maiduguri da kamfanin TCN tayi, yan ta’addan Boko Haram sun sake lalata wayoyin isar da lantarki na Damaturu-Maiduguri.
Daily Trust ta ruwaito cewa wani babban jami’in TCN ya tabbbatar da hakan da yammacin Asabar.
Read Also:
“Bayan kokarin da kamfanin TCN tayi na gyara wutan lantarkin Maiduguri, birnin jahar Borno, yan ta’addan sun sanya Bam a layin wutan 152 da 153 (Molai) 330kv dake Damaturu-Maiduguri misalin karfe 5:56 na safiyar 27 ga Maris, 2021, inda suka jefa garin Maiduguri cikin duhu karo na biyu,” jami’in ya bayyana.
Wannan ba shine karo na farko da yan ta’addan Boko Haram zasu jefa mutan Maiduguri cikin duhu ba.
A watan Junairu, yan ta’addan Boko Haram sun lalata wani layin da ya jawo lantarki zuwa cikin jahar Borno.
Harin na ranar 26 ga watan Junairu shine na uku a cikin watan wanda mayaƙan dake ikirarin kafa ƙasar musulunci (ISWAP) ta kai garin, kuma ya yi sanadiyyar ɗaukewar wutar gaba ɗaya.
Amma da yammacin Laraba, 24 ga Maris, mazauna garin Maiduguri sun ɓarke da murna da da suka ga hasken wutar lantarki ya dawo a yankin su.