Wani Mutum ya Samu ‘Yanci Bayan Shekaru a Gidan Yari

Wani mutumin jihar Michigan a kasar Amurka, ya samu yanci bayan kwashe kimanin shekaru 40 a gidan yari kan laifin da bai aikata ba.

A cewar CNN, mutumin mai suna Walter Forbes ya samu yanci ne bayan matar da tayi shaida kansa ta janye maganarta saboda karya tayi.

Walter Forbes, wanda ke da shekaru 63 yanzu, ya shiga kurkuku ne yana dalibin jami’a mai shekaru 25, bayan zarginsa da kisan Dennis Hall, a shekarar 1982, ABC ta ruwaito.

Budurwa yar shekara 19 a lokacin, Annice Kennebrew, ta bada shaidan cewa ta ga Walter Forbes da wasu mutane biyu dauke da galolin mai suna watsawa a gidan, bisa rahoton da CNN ta samu.

Cikin su ukun da akayi zargi da bankawa ginin wuta wanda yayi sanadiyar mutuwar Dennis Hall, Forbes kadai aka kama da laifi, CNN ta kara.

Bayan shekaru 30 a kurkuku, mutumin ya tuntubi kungiyar kwato hakkin wadanda aka yiwa sharri, Michigan Innocent Project, kuma aka fara binciken lamarin a 2010.

Bayan shekaru bakwai a 2017, budurwar da bada shaida kansa a kotu, Annice Kennebrew, ta amince da tattaunawa da lauyan Forbes inda ya bayyana cewa an tilasta ta yi masa shaidan karya ne.

“Sun yi barazanar kashe yarana, iyayena, ‘yan uwana, da ni idan ban kai kara ofishin yan sanda kuma na bada shaida a kotu ba cewa na ga Walter da wasu mutane biyu suna banka wuta,” ta fadi a wani takardar da CNN ta samu.

“Duk abubuwan da na fada, duk shaidun da na basa game da gobarar karya ne,” ta kara.

“A iyakan sani na, Walter bai da hannu cikin laifin.”

Yayinda aka koma kotu a watan Yuni, Kennebrew ta ce ta bada shaida kansa lokacin ne saboda lokacin karamar yarinya ce mai yara kuma tana tsoro, a cewar ABN.

An saki Walter Forbes daga gidan yari ranar 20 ga Nuwamba.

“Babu wani bakin cikin da zanyi da ita kuma na yafe mata saboda ita ma tilasta ta akayi,” yace.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here