‘Yan Daba Sun Kai wa Jami’an Hukumar Kwana-Kwana Hari a Jahar Kogi
‘Yan daba sun kai wa wasu jami’an hukumar kwana-kwana farmaki a Lokoja, jahar Kogi inda suka ji masa miyagun raunuka.
Jami’in hulda da jama’an hukumar ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranara Juma’a
A cewar sa an kira hukumar su don kashe wata gobara ne, suna isa ‘yan daba suka far musu da makamai.
Kogi – Wasu ‘yan daba sun kai wa jami’an hukumar kashe gobara farmaki a Lokoja, jahar Kogi, inda suka yi musu kaca-kaca da makamai, Daily Trust ta rawaito.
Jami’in hulda da jama’an hukumar, Ugo Huan, ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Juma’a wacce ya gabatar wa da manema labarai.
Yadda lamarin ya faru
Read Also:
Kamar yadda Daily Trust ta rawaito, takardar ta bayyana cewa lamarin ya auku ne a ranar Laraba akan titin Felele lokacin da jami’an hukumar kwana-kwanan suka nufi inda gobara ta kama wata mota a gidan man Al-Salam dake kallon Kogi State Polytechnic.
Bayan an kira hukumar an sanar da su cewa gobara ta kama wata mota, isar su ke da wuya suka ga ‘yan daba sun fara kai musu farmaki da makamai. Sai da suka lalata babbar motar su sannan suka ji wa jami’an hukumar raunuka, yanzu haka suna asibiti ana kulawa da lafiyar su.
Ba wannan bane karo na farko da hakan ya faru ba.
“Wannan ne karo na biyu a jahar Kogi da ake kai wa jami’an hukumar kwana-kwana farmaki,” kamar yadda takardar tazo.
‘Yan sanda suna bincike akan lamarin.
Daily Trust ta rawaito yadda Huan da kanshi yace an kai wa ‘yan sanda rahoto kuma suna bincike don kamo duk wadanda suke da hannu a lamarin.
Shugaban hukumar kwana-kwana, Dr Liman Ibrahim, ya yi alawadai da farmakin kuma ya lashi takobin tabbatar da an kama wadanda suka yi wannan aika-aika an hukunta su.
Kamar yadda shugaban hukumar ya ce:
“Jami’an zasu dakatar da aikin su ga duk gwamnatin jahar da ba za ta iya kulawa da rayukan jami’an hukumar da kayan aikin su ba.”