Ambaliyar Ruwa: ‘Yan Gudun Hijira 6,830 Dake Bakassi Sun Rasa Matsugunni
Rahotanni sun tabbatar da yadda ruwan saman da aka yi ranar Talata da yamma yayi sanadiyyar rasa matsugunnin ‘yan gudun hijira.
Ruwan da aka yi kamar da bakin kwarya ya rutsa da kimanin ‘yan gudun hijira 6,830 dake zaune a sansaninsu na Bakassi.
Sun shiga tsaka mai wuya sakamakon rashin makwanci da kuma fargabar barkewar annobar cutar kwalara da ta yawaita a garuruwa.
Bakassi, Borno – Dubban ‘yan gudun hijira dake jahar Borno sun shiga tsaka mai wuya sakamakon mamakon ruwan sama da ya barke a ranar Talata da yamma.
Rahotanni sun tabbatar da yadda aka tafka ruwa kamar da bakin kwarya wanda yayi ta ambaliya a yankin, Daily Trust Aminiya ta ruwaito.
‘Yan gudun hijirar sun shiga mummunan yanayi akan rashin wurin kwana da fargabar barkewar annobar kwalara, Daily Trust Aminiya ta ruwaito.
Read Also:
An samu tattaunawa da wasu daga cikin ‘yan gudun hijirar inda aka gano cewa ruwa ya mamaye ofisoshi da duk wasu matsugunai da kungiyoyi suka agaza suka gina musu.
Dalla-dalla yadda lamarin ya auku.
Daya daga cikin ‘yan gudun hijirar, Bura Kaka ya yi kira ga gwamnati da sauran kungiyoyi da su taimaka su gina musu matsugunnin da zasu raba a Bakassi.
Tun karfe 4:50 na yamman ranar Talata ruwa ya barke mai yawa kamar da bakin kwarya. Hakan ya janyo ambaliya musamman ga masu kwana a tantina.
Gaba daya sansanin ya cika makil da ruwa. Muna bukatar taimako na gaggawa daga gwamnati da sauran kungiyoyi masu zaman kansu da su taimaka mana don har yanzu ba a gama ruwan ba.
Muna rokon masu hannu da shuni da gwamnati ta kalli mummunan yanayin da muke ciki da kuma barkewar cutar kwalara da zazzabun cizon sauro da yake ta bulla wuri-wuri ta agajemu,” a cewar Kaka.
Bayan aukuwar lamarin, wani jami’in hukumar bada agaji cikin gaggawa ta kasa (NEMA), ya tabbatar da cewa hukumarsu tare da hadin kan SEMA ta jahar sun hada karfi da karfe wurin kai dauki ga ‘yan gudun hijirar dake Bakassi.