Hukuncin da Kotu ta Yanke wa ɗan Abdulrasheed Maina, Faisal Maina

 

Wata babbar kotun tarayya a babban birnin Najeriya Abuja ta yanke wa Faisal, ɗan Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar sauye-sauye ta fansho hukuncin ɗaurin shekara 24 a gidan yari, kamar yadda gidan talabijin na ƙasar NTA ya rawaito.

A yayin yanke hukuncin a ranar Alhamis, Mai Shari’a Okon Abang ya samu Faisal da laifuka uku da suka haɗa da halatta kuɗin haram, wanda hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati EFCC ra tuhume shi da su.

Mai Shari’a Abang ya ce EFCC ta gabatar da hujjojin da ke tabbatar da cewa Faisal ya yi amfani da wani asusun ajiya na banki na gaibu a bankin UBA, inda ta can ne mahaifinsa Maina ya yi zambar kudi har naira miliyan 58.1.

Kotun ta ce an tura kuɗin ne asusun mai ɗauke da sunan Alhaji Faisal Farm 2, kuma Faisal da mahifinsa sun cire kuɗaɗen daga tsakanin Oktoban 2013 zuwa Yunin 2019.

Faisal bai halarci zaman kotun ba, ana zargin ya tsere daga ƙasar tun tuni.

Mai shari’ar ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 14 ne kan laifuka biyu sai kuma shekara goma kan laifuka biyu.

An yanke wa Faisal hukuncin shekara 24 ne amma zai yi zaman gidan kaso na shekara 14 ne.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here