Yankuna da Jahohin da Suka fi Samun Wakilai a Nade-Naden Shugaba Buhari
Biyo bayan zargin da Bishop Mathew Kukah yayi wa Shugaban kasa Muhaammadu Buhari na son kai, an koma ga tattauna wasu yankuna ne suka fi samun wakilai a nade-naden Shugaban kasar.
Wannan zauren ya kawo bayani dalla-dalla kan nade-nade 190 da Buhari yayi a kwanaki kamar yadda jaridun Premium Times da Daily Trust suka ruwaito.
Jaridun biyu sun yi nuni ga wata takarda daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya.
Rabe-raben yanki-yanki
1. Kudu maso yamma – Nade-nade 64
2. Arewa maso yamma – Nade-nade 37
3. Arewa maso gabas – Nade-nade 29
4. Kudu maso kudu – Nade-nade 24
5. Arewa maso tsakiya – Nade-nade 21
6. Kudu maso gabas – Nade-nade 15
Read Also:
A matakin jaha, jahar Ogun ce ke da mukaman siyasa mafi yawa da Shugaban kasa Buhari nada tun bayan sake zabensa a 2019 inda take da 17 cikin nade-nade 190 a daidai lokacin wannan rahoton. Kalli rabe-rabensu a kasa.
Rabe-raben Jiha-jiha: Guda biyar da ke kan gaba
1. Jahar Ogun – 17
2. Jahar Adamawa – 14
3. Jahar Kano – 12
4. Jahar Lagos – 12
Dalla-dalla: Kudu da Arewa
1. Yankin kudu (jahohi 17) – Nade-nade 103
2. Yankin Arewa (jihohi 19) – Nade-nade 87
Legit.ng ta tattaro cewa dukkanin nade-naden na aiki a ofishoshin Shugaban kasa, mataimakin Shugaban kasa, uwargidar Shugaban kasa da uwargidar mataimakin Shugaban kasa.
Premium Times ta nusar cewa dakatar ofishin sakataren gwamnatin bai sanya nade-naden da Shugaban kasar yayi a ma’aikatun tarayya (sakatarorin dindindin), hukumomi da masana’antu ba.
Hakazalika ba ya dauke da nade-naden jakadu da na hukumomin tsaron kasar.