‘Yan Majalisa ba sa Rayuwar Jindadi- Benjamin Kalu
Honarabul Benjamin Kalu ya bayyana dalilin da ya sa yan majalisa ke yawan mutuwa yanzu.
.
Dan majalisan ya bayyana cewa yan Najeriya musamman mutan mazabunsu na damunsu da yawa.
Yan bayyana cewa yan majalisan ba sa wani rayuwan jin dadi.
Yan majalisai dokokin tarayyan Najeriya ne mafi fama da talauci a duniya, mai magana da yawun majalisar wakilai, Benjamin Kalu, ya bayyana.
Kalu ya bayyana haka ne yayin amsa tambaya kan zargin da ake yiwa wasu yan majalisa na amsan rashawa, The Nation ta ruwaito.
Ya yi watsi da zarge-zargen inda ya ce annobar COVID-19 ce ta janyo musu jinkiri wajen kammala bincike-bincike.
Read Also:
Kalu ya kara da cewa yan majalisa na rashin lafiya ne saboda irin wutan da yan Najeriya kunna musu.
“Kan maganan rashawa, ai da kun gani a jikin yan majalisa. Wannan shine majalisa mafi fama da talauci.Ba za ku ga yan majalisa na rayuwan jin dadi ba. Wani kudi zasu sata? Wahala kawai muke sha,” Kalu yace.
“Dalilin da yasa yawancin yan majalisan dake mutuwa ciwon zuciya ke kashe su Wahalan da mutanen mazabunsu ke basu yayi yawa.”
“Maganar gaskiya itace, ko ku fahimta ko ku ki. Wahalan da mutanenmu ke bamu yake kashe yan majalisar dokokin tarayya. Wannan shine gaskiya. Wahalan yayi yawa,” ya kara.
Daga 2019 zuwa yanzu, Sanatoci 4 da yan majalisar wakilai 3 suka mutu. A 2020, N125 billion aka baiwa yan majalisan yayinda suka samu N134 billion a kasafin kudin 2021.