APC: ‘Yan Majalisa Shida na Jahar Ogun Sun Koma Jam’iyyar

‘Yan majalisa shida tare da shugaban marasa rinjaye na jahar Ogun ne suka koma jam’iyyar APC.

Kakakin majalisar ya sanar da hakan a zaman majalisar na ranar Alhamis a wasiku mabanbanta.

Sun ce komawarsu jam’iyyar mai mulki ya biyo bayan tuntubar shugabanni da magoya bayansu.

‘Yan majalisa bakwai na jahar Ogun da suka hada da shugaban marasa rinjaye, Ganiyu Oyedeji ne suka bar jam’iyyar APM zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Kakakin majalisar jihar, Olakunle Oluomo, ya bayyana haka a wasu wasiku mabanbanta da ya karanta yayin zaman majalisar a ranar Alhamis a Abeukuta, babban birnin jihar, Punch ta wallafa.

Wadanda suka sauya shekar baya da Oyedeji: Musefiu Lamidi (Ado Odo Ota 11), Yusuf Amosun (Ewekoro), Sikiratu Ajibola (Ipokia), Bolanle Ajayi (Yewa South), Adeniran Ademola (Sagamu 11) da Modupe Mujota-Onikepo (Abeokuta North).

A wasiku mabanbanta na ‘yan majalisaru, sun ce sun yanke shawarar komawa jam’iyyar APC bayan tuntubar shugabanninsu da magoya bayansu.

A martanin kakakin majalisar, ya taya ‘yan majalisar murna da suka koma jam’iyyar mai mulki tare da cewa hakan yana da matukar amfani domin ganin cigaban jihar baki daya.

Oluomo ya yi kira ga shugaban marasa rinjaye na majalisar da ya dauka babban matakin komawa jam’iyya mai mulki.

Bayan sauya shekar a yau, APC tana da mambobi 22 daga cikin 26 na majalisar. ADC tana da mambobi 3 sai PDP da ke da 1.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here