Ƴan Majalisar Tarayya 2 sun Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC

 

FCT Abuja – Ƴan Majalisar wakilan tarayya biyu sun sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki a zamansu na yau Talata, 18 ga watan Maris, 2025.

Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ne ya karanta wasikun da ƴan Majalisar suka rubuto domin tabbatar da komawarsu jam’iyyar APC.

Hakan na kunshe ne a wani faifan bidiyo da Imran Muhammad, wani mai amfani da kafar sada zumunta ya wallafa a shafinsa na X watau Tuwita.

Ƴan Majalisar Wakilai 2 sun koma APC

Waɗanda suka sauya shekar sun haɗa da Hon. Hussaini Mohammed Jallo, mamba mai wakiltar mazaɓar Ugabi ta jihar Kaduna.

Sai kuma Hon. Adamu Tanko, mamba mai wakiltar mazaɓar Gurara/Suleja/Tafa ta jihar Neja da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya.

Hon. Jallo Hussaini da Hon. Adamu Tanko, sun mika wasikun murabus dinsu daga PDP, tare da sanar da sauya sheƙa zuwa APC a hukumance a zaman Majalisa na yau Talata.

Sauya shekar wadannan ‘yan majalisa ya kara rage karfin jam’iyyar PDP a majalisar wakilai yayin da ita kuma APC ta samu ƙaruwar mambobinta.

Kakakin Majalisa ya taya su murna

Wannan mataki na iya tasiri a siyasar majalisar, musamman a bangaren yanke manyan hukunci da zartar da kudurori masu muhimmanci.

Da yake karanta wasikar ɗan Majalisar mai wakiltar Igabi, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya taya masu sauya sheƙar murna tare da yi masu maraba da zuwa jam’iyya mafi girma a Afirka.

“Ina maku maraba zuwa jam’iyya mafi girma a Afirka, jam’iyyar kawo sauyi da ci gaban ƙasa,” in ji Tajudeen Abbas.

Me ya sa ƴan Majalisar suka koma APC

A wasiƙar sauya shekarsa, Hon. Hussaini Mohammed ya bayyana cewa ya yanke shawarar komawa APC ne saboda rikicin da ya ƙi ci kuma ya ƙi cinyewa a PDP.

Hussaini, wanda shi ne dan majalisa na biyu a PDP daga jihar Kaduna da ya koma APC, ya ce kalubalen da ake fuskanta a jam’iyyar ya yi tsananin da ba zai iya ci gaba da zama ba.

A nasa ɓangaren, Hon. Adamu Tanko ya ce ya tuntubi jama’ar mazabarsa tare da yanke shawarar sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Shugaban marasa rinjaye a Majalisar Wakilai, Hon. Kingsley Chinda ya yi fatali da sauya shekar ƴan Majalisar, ya ce ƴan adawa ba za su gaji da nuna ɓacin ransu ba sai an yi abin da ya dace.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here