‘Yan Majalisa Sunyi Tir da Kasafin Kudin 2021

 

Majalisa tana ganin Naira Biliyan 45 sun yi wa yankin Arewa maso gabas kadan.

‘Yan Majalisar Tarayya na so a kara kason yankin a kundin kasafin kudin 2021.

Zainab Gimba ta ce sam babu adalci a kason da gwamnatin shugaba Buhari tayi.

A ranar Talata, 8 ga watan Disamba, 2020, ‘yan majalisar wakilan tarayya su kayi tir da kason da aka gutsura wa yankin Arewa maso gabas a kasafin kudi.

‘Yan majalisar suna ganin Naira biliyan 45.32 da gwamnatin tarayya ta ware domin yi wa daukacin yankin abubuwan more rayuwa a 2021, sun yi kadan.

Jaridar Vanguard ta ce har ila yau, ‘yan majalisar suna ganin kason hukumar NEDC mai kula da cigaban yankin na Arewa maso gabas ba zai iya wani tasiri ba.

Honarabul Zainab Gimba mai wakiltar yankin Borno ta gabatar da korafi yayin da ta mike a zauren majalisar a ranar Talata, tana neman a gyara kasafin kudin.

Zainab Gimba tace tattalin arzikin yankinsu ya shiga halin ha’ula’i a sakamakon rikicin Boko Haram, don haka ake bukatar a narka kudi a wannan shiyya.

Gimba tace ta’adin Boko Haram sun hada da rusa hanyoyi, makarantu da jawo karancin abinci.

A karshe, majalisar wakilan ta amince da cewa shugabannin kwamitocin kudi, kasafi da na NEDC su zauna da gwamnatin tarayya domin a kara kason yankin.

Hon. Gimba ta kuma tado batun kudin da aka ware saboda annobar COVID-19, ta ce kason yankinta Arewa maso gabas ya yi kadan, ba ayi masu adalci ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here