Gwamna Yahaya Bello ya yi Kira ga ‘Yan Najeriya da su Duba Cancanta a Zaben 2023

 

Gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello ya shawarci ‘yan Najeriya da su duba cancanta ba yanki ba wajen zaben shugaba.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin wani taron da ya gudana jiya Talata a jahar Nasarawa, Lafiya.

Gwamnan ya ce, ya kamata a ba matasa damar rike madafun iko a zaben shekarar 2023 mai zuwa.

Nasarawa – Gwamnan jahar Kogi, Yahaya Bello, ya ce cancanta ya kamata ya zama babban abin da ‘yan Najeriya za su fi mayar da hankali a kai, yayin da suke zuwa rumfunan zabe don zaben wanda zai maye gurbin Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), a 2023.

Ya fadi haka ne a jawabin da Shugaban Ma’aikatansa, Mohammed Abdulkareem ya yi a madadinsa a wani taron kwanaki biyu na jagorancin kasa kan zaman lafiya da tsaro da Majalisar Matasan Najeriya ta shirya.

An gudanar da shirin ne a jahar Nasarawa, Lafia ranar Talata 17 ga watan Agusta, jaridar Punch ya ruwaito.

Yahaya ya bukaci shugabannin siyasa na kasar nan da su ba matasa dama don daukar matsayin shugabanci a 2023.

Gwamnan ya ce:

“Zabin wanda zai zama Shugaban Najeriya na gaba a 2023 dole ne ya dogara da wanda ya dace ba wai yankin da ya fito ba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here