‘Yan Najeriya Sun Gaji da Jam’iyyar APC Mai Mulki – Kwankwaso

 

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP ya kai ziyarar bude ofishin jiha a Gombe, ya yi maganganu masu dauakr hankali.

Kwankwaso, wanda ya samu tarba daga Gombawa ya bayyana jin dadinsa tare da fadin shirye-shiryensa na 2023.

Ya kuma ce, alamu masu karfi sun nuna cewa, ‘yan Najeriya sun kagu da ganin karshen mulkin Manjo Muhammadu Buhari mai ritaya.

Jihar Gombe – Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Alhaji Rabi’u Kwankwaso, ya ce daga dukkan alamu ‘yan Najeriya sun gaji da jam’iyyar APC mai mulki, kuma suna da burin ganin karshen gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kwankwaso ya yabawa dimbin jama’a da suka fito domin tarbarsa a jihar Gombe da yammacin ranar Asabar, inda ya bayyana hakan a matsayin wata alama da ke nuna cewa jama’a a shirye suke don samun damar kawar da gwamnatin APC a zaben 2023.

Kwankwaso, wanda ya je Gombe domin kaddamar da ofishin jam’iyyar, ya ce dimbin jama’a da suka fito domin tarbarsa daga filin jirgin sama zuwa cikin garin, sun zaburar da shi cewa jihar Gombe ta shiga sahun su Kano wajen jihohin Kwankwasiyya.

Da yake jawabi ga magoya bayansa a otal din Gombe na kasa da kasa, jim kadan bayan kaddamar da ofishin, Kwankwaso ya ce akwai manyan alamu na kyakkyawar makoma ga jam’iyyar da ba ta kai watanni hudu ba da yin kaurin suna.

A cewarsa, NNPP za ta kawo wa ‘yan Najeriya sauyi mai kyau ta hanyar share hawaye da wahalhalun da gwamnatin Buhari ta sanya su, inji rahoton gidan talabijin na Arise.

A cewarsa:

“Jami’an gwamnatin APC masu hadama sun durkusar da duk wani bangare na tattalin arzikin Najeriya, in ban da aljihunsu.”

Ya kuma bukaci jama’a da su fito su karbi katin zabensu na dindindin (PVCs), domin hakan ne kawai zai kai ga kawo sauyi a kasar.

NNPP za ta kawo wuta a zaben 2023, Buba Galadima

A nasa jawabin, shugaban kwamitin amintattu na NNPP, Buba Galadima, ya ce zaben 2023 zai yi wa jam’iyyar NNPP murmushi, ganin yadda aka karbe su a jihar Gombe, rahoton Tribune Online.

Galadima ya yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da su je su nemi katinan su na PVC tare da jan hankalin ‘yan Nijeriya a duk sassan jihar, musamman a kauyuka da su ma su yi hakan.

Dan takarar gwamna na jam’iyyar a jihar, Alhaji Ahmed Mailantarki, ya godewa dan takarar shugaban kasa bisa ziyarar da ya kai masa, ya kuma ba shi tabbacin cewa ofishin jam’iyyar zai kara inganta ayyukan yakin neman zabensu a Gombe.

Mailantarki ya ce jam’iyyar NNPP a jihar Gombe ta dogara sosai ga ikon talakawa, wadanda su ne kashin bayan jam’iyyar.

Ya ce NNPP ta samu goyon bayan al’ummar Gombe ne saboda sun bi sahun Kwankwaso, wanda ya baiwa matasa damar cikar burinsu da kuma damar da suke da ita a bangarori daban-daban.

A kalamansa:

“Ta hanyar kwaikwayar abubuwan da ka gada, mun sami damar tura wasu matasa ‘yan Najeriya takwas zuwa Turai da sauran sassan duniya domin cika burinsu na kwallon kafa, kuma har yanzu muna shirin kara habaka irin wannan shiri.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here