‘Yan Najeriya Sunyi Martani a Kan Gwamnonin da Suka Halarci Bikin ‘Dan Malami Maimakon Jana’izar Janar Ibrahim Attahiru

 

‘Yan Najeria sun fusata yayin da wasu gwamnoni suka halarci bikin dan Malami maimakon jana’izar COAS.

Wasu sun bayyana fushinsu a shafin Tuwita inda suka ce gwamnonin basu kyauta ba kwata-kwata.

Sai dai, an samu wasu gwamnonin da suka halarci jana’izar da aka yi jiya Asabar a babbanin tarayya Abuja.

Yayin da ake jana’izar Janar Ibrahim Attahiru, Shugaban hafsan soji, da wasu 10 da suka mutu a hatsarin jirgin sama a Abuja, gwamnoni da yawa sun hallara zuwa Kano don halartar bikin dan Abubakar Malami, Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a.

Wannan ya haifar da cece-kuce daban-daban daga ‘yan Najeriya wadanda ke ganin manyan hafsoshin sojojin da suka mutu a bakin aiki ba su sami irin girmamawar da ta dace da su ba.

Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ba su halarci jana’izar ba wacce ta samu halartar Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan. Bayan hadarin jirgin a ranar Juma’a, Malami ya fidda da sanarwa, yana cewa ya katse auren dansa, Daily Trust ta ruwaito.

Amma an yi ta shagulgula da annashuwa a Kano lokacin da aka daura auren Abiru Rahman Malami a masallacin Juma’a na Alfurqan da ke cikin garin na Kano.

Daga cikin gwamnonin da suka halarci daurin auren sun hada da Bello Matawalle (Zamfara), Aminu Tambuwal (Sokoto) Inuwa Yahaya (Gombe), Abdullahi Ganduje (Kano) da Atiku Bagudu (Kebbi).

Halartar bikin da gwamonin suka yi maimakon zuwa wajen jana’izar ya jawo cece-kuce yayin da ‘yan Najeriya ke nuna fushinsu a shafukan sada zumunta. Tsohon dan takarar shugaban kasa a Najeriya, Adamu Garba II, ya wallafa a Tuwita cewa:

“Idan da gaske ne cewa a lokacin Najeriya ke cikin wani jimamin rashin fitaccen jaruminmu, Janar Attahiru, amma wasu Gwamnonin Arewa sun shagala da bikin daurin auren wani dan babban Lauyan Janar/Ministan Shari’a, a Najeriya, to wannan masifa biyu kenan.

“Janar Attahiru da tawagarsa su suke aiki ba dare ba rana ba tare da kakkautawa ba don samar da tsaron rayuka da kadarori ga wasu jihohin da wadannan Gwamnonin suke mulka.

“Mafi qarancin bashin da yake binsu shine girmamawa ta karshe daga ranar sa ta karshe a duniya, bayan fitaccen aiki da jarumtaka.

“Abin kunya!”

Maybeks ya rubuta a Tuwita: “Yayin da kasa ke juyayin mutuwar COAS da wasu hafsoshin soja, wasu Gwamnonin Arewa da abokan AGF, Malami sun hallara a Kano don bikin auren dansa.”

FS Yusuf ya ce:

“Sojoji ne dalilin da yasa muka iya yin zabe a Arewa wanda ya kawo wadannan wawayen kan mulki. “A yau, ba za su iya halartar jana’izar COAS ba amma sun hallara don bikin auren dan Malami mai shekaru 21. Wadannan su ne mutanen da aka zaba.

Ban san abin da zan kira kuduka ba!”

Shi kuwa Kwakwason Tuwita cewa yayi:

“Akwai wani abu da ake kira yanayin da kasa ke ciki,” “Hoto na 1: Wike ya gudanar da taron siyasa yayin da Najeriya ke juyayin mutuwar marigayi shugaban sojoji, da wasu.

“Hoto na 2: Gabanin bakin cikin da kasa ke ciki, gwamnonin Najeriya, ministoci, ‘yan majalisa sun halarci daurin auren dan Malami.”

Duk da haka, wasu manyan jami’an gwamnati sun karrama jami’an da suka mutu tare da kasancewarsu a wajen jana’izar.

Daga cikinsu akwai Gwamnoni irinsu Babagana Zulum (Borno), Nasir El-Rufai (Kaduna) da Mai Mala Buni (Yobe). Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed; Ministan Tsaro, Bashir Magashi; da Shugaban Ma’aikata na Shugaba Muhammadu Buhari, Farfesa Ibrahim Gambari su ma suna wurin. Yayin da Shugaban Rundunar Tsaro, Janar Lucky Irabor da Shugaban Sojojin Ruwa, Rear Admiral Awwal Gambo, Mukaddashin IGP, Usman Baba, su ma suka halarci bikin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here